Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Gidauniyar Ɗanbayo ta ƙaddamar da wani shirin tallafa wa ilimi da zai shafi kusan ɗalibai 83,000 da malamai 415 a makarantu 83 da ke faɗin Jihar Gombe, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo.
An ƙaddamar da shirin ne ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, 2026, a Makarantar Alabura S. Kudin Model Nursery, Primary and Junior Secondary School da ke Kumbiya-Kumbiya, Gombe, inda gidauniyar ta raba kayayyakin karatu daban-daban ga makarantar.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da littattafan rubutu, kundin rajistar aji, littattafan tsara darasi, alƙaluman rubutu, masu auna layi, fensir, masu goge rubutu, dastar goge allo da sauran kayan karatu.
Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya kafa gidauniyar, Ambasada Yusuf Musa Danbayo, ya ce an samar da shirin ne bisa ɗabi’un taimakon jama’a da kuma gadon kyakkyawan aiki da marigayi mahaifinsa ya bari.
Ya ce ilimi na daga cikin manyan jari da ake iya ginawa domin samun kyakkyawar makoma ga al’umma, yana mai cewa samar wa ɗalibai kayan karatu na yau da kullum na iya taimakawa wajen rage wasu daga cikin ƙalubalen da ke kawo cikas ga karatunsu.
Danbayo ya ce gidauniyar ta fara ayyukan jinƙai ne a shekarar 2004, inda ta fara da kare muhalli da dashen itatuwa, kafin ta faɗaɗa ayyukanta zuwa fannin ilimi a shekarar 2005.
A cewarsa, gidauniyar ta tallafa wa yara daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar taimaka musu shiga makaranta, samar musu da kayan makaranta da littattafan rubutu, da kuma taimakawa wajen biyan wasu buƙatun Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA).
Ya ce sabon shirin na da nufin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati a fannin ilimi, tare da ƙarfafa wa ɗalibai gwiwar ci gaba da zuwa makaranta duk da matsalolin tattalin arziki.
Ɗanbayo ya yi kira ga iyaye da su ƙara ba da muhimmanci ga karatun ’ya’yansu, yayin da ya buƙaci malamai su ci gaba da jajircewa wajen haɓaka ilimin ɗalibai da kuma tarbiyyarsu.
Ɗanbayo ya ce sabon shirin wata hanya ce ta ci gaba da kiyaye kyakkyawan gadon marigayi mahaifinsa na hidimtawa al’umma, tare da ƙarfafa gwiwar mutane da ƙungiyoyi su ƙara bayar da gudummawarsu wajen ci gaban al’umma.
Ya kuma shawarci ɗaliban da suka amfana da tallafin da su kasance masu ladabi, ƙwazo da mai da hankali kan karatunsu, yana mai tabbatar musu cewa halin da suke ciki a yanzu bai kamata ya zama abin da zai ƙayyade makomarsu ba.
Sakataren Ilimi, na ƙaramar hukumar Gomhe Abubakar A. Baba, ya yabawa gidauniyar bisa tallafa wa makarantu da kuma ƙoƙarin da take yi na ƙara wa gwamnati ƙarfi wajen inganta ilimin bai ɗaya a jihar.
Baba ya ce tallafin da gidauniyoyi, ɗaiɗaikun mutane da sauran ƙungiyoyi ke bayarwa na iya taimaka wa makarantu wajen magance wasu daga cikin buƙatunsu na gaggawa, musamman wajen samar da kayan koyarwa da na koyo.
Ya buƙaci ɗaliban da suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, tare da mai da hankali kan karatunsu.
Shi ma wakilin Kwamishinan Ilimi ya yaba wa wannan shiri, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki waɗanda ba na gwamnati ba na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa fannin ilimi.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni, kamfanoni, gidauniyoyi da sauran masu kishin al’umma da su yi koyi da wannan ɗabi’a ta hanyar tallafa wa makarantu da yara, musamman waɗanda suka fito daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Shugaban Makarantar Alabura S. Kudin Model School ya nuna godiyarsa ga gidauniyar, yana mai cewa tallafin zai samar da muhimmiyar gudummawa ga malamai da ɗalibai.
Ya ce kayayyakin za su taimaka wajen samar da ingantaccen yanayin koyo, inda ya roƙi gidauniyar da ta ci gaba da shirin.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka amfana da tallafin sun kuma nuna godiyarsu, inda suka ce kayayyakin za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukan aji tare da rage musu wahalhalun samun kayan karatu na yau da kullum.
Sun kuma yi kira ga sauran gidauniyoyi, ƙungiyoyi da daidaikun mutane da su tallafa wa makarantu da ɗalibai, musamman yara daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Taron ya samu halartar jami’an ilimi, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, jami’an tsaro, malamai, ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki.
Gidauniyar, wadda taken ta shi ne “ƙarfafa hankula, kare rayuka, hidimtawa Bbil’adama da gina makoma mai ɗorewa,” ta ce ayyukanta sun shafi tallafin jin ƙai, kare muhalli, kiwon lafiya, tsafta da bunƙasa al’umma, baya ga fannin ilimi.
