
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Ƙolin Shari’a ga Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasa (NSCIA) ta ce ta sabunta tare da faɗaɗa tsarin Majalisar Zartarwarta ta Ƙasa (NEC).
A wata sanarwa da Jami’in hulɗa da jama’arta, Abbas Jimoh ya fitar a ranar Asabar, ya ce matakin ya biyo bayan matsayar da aka cimma ne a Babban Taron NSCIA da aka gudanar a ranar Juma’a, 1 ga October. Ya ce taron ya samu halartar jagororin Islama, ciki har da sarakunan gargajiya musulmi da manyan limaman masallatai a faɗin jihohi 36 da Abuja.
A cewarsa, majalisar ta amince da sabuntawa da faɗaɗa tawagar jagororinta na ƙasa, inda ta naɗa Mahfouz Adedimeji a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Ƙasa, Salisu Shehu a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Ƙasa-da-ƙasa, Abeny Mohammed a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Haɗaka, da kuma Bala Muhammad a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Gudanarwa.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Umar Jibrilu Gwandu a matsayin Jami’in Yaɗa Labarai (PRO) na Ƙasa da Hajia Sekinat Lawal a matsayin Mataimakiyar Jami’in Yaɗa Labarai (DPRO). Haka kuma an naɗa Mairo Mandara a muƙamin Jami’iar Ci-gaba yayin da aka naɗa Abdullahi Musa PenAbdul a matsayin Mataimakin Jami’in Ci-gaba (Dabaru). Sai Fatimah Abdulkarim a matsayin Jami’ar Harkokin Cikin Gida.
Hakan na zuwa ne yayin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban NSCIA, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga a martaba addini a babban taron. Ya bayyana cewa, babu wanda za a tilasta wa shiga Musulunci, yana mai cewa ya dace Musulmi su riƙa girmama sauran ‘yanci da addinan wasu mutane.
