Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Wani malami a jami’ar Jihar Gombe (GSU), Farfesa Matthew F. Bello, ya yi kira da a sake fasalin tsarin aikin gwamnati a Najeriya domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da manufofi da samar da ayyukan da za su amfani ’yan ƙasa.
Bello, wanda shi ne shugaban sashen kula da harkokin gwamnati na GSU, ya bayyana hakan ne a taron kasa da kasa na biyu da sashen ya shirya, mai taken, “Dimokuraɗiyya, aikin gwamnati da samar da ayyuka a Najeriya: Tsara ajandar babban zaɓen 2027.”
Ya ce duk da sauyin gwamnati da ka iya biyo bayan babban zaɓen 2027, ma’aikatan gwamnati za su ci gaba da kasancewa ginshiƙin aiwatar da manufofi da shirye-shiryen kowace gwamnati.
A cewarsa, akwai buƙatar a samar da tsarin aikin gwamnati da zai bai wa ma’aikata damar gudanar da ayyukansu cikin kwarewa, riƙon amana da kishin ƙasa, domin sauya manufofin gwamnati zuwa ayyukan da jama’a za su iya gani da amfana da su.
“Ma’aikatan gwamnati da jami’an gwamnati za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa a gwamnati mai zuwa. Wannan ne ya sa muka shirya wannan taro domin tattauna yadda za a sake fasalin aikin gwamnati domin ya sauke nauyin aiwatar da manufofi da samar da ayyukan da za su inganta rayuwar ’yan kasa,” in ji shi.
Bello ya ce taron ya haɗa masana, ’yan siyasa, ma’aikatan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin duba ƙalubalen da ke hana aikin gwamnati samun ingantaccen sakamako, tare da tattauna hanyoyin da za a bi wajen inganta shugabanci da samar da ayyuka.
Ya kuma buƙaci gwamnatoci da su tabbatar da dorewar manufofi da shirye-shiryen da suka amfani jama’a, maimakon dakatar da su saboda sauyin shugabanci.
Malamin ya jaddada buƙatar ƙarfafa hukumomin gwamnati da kuma amfani da bincike da hujjoji wajen tsara manufofi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da matakan da suka dace da buƙatun al’umma.
Ya kuma bayyana jami’o’i a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen inganta shugabanci, ta hanyar gudanar da bincike, samar da sabbin dabaru da haɗa masana da masu tsara manufofin gwamnati.
Bello ya bayyana fatan cewa shawarwarin da za su fito daga taron za su taimaka wajen sake fasalin aikin gwamnati da inganta tsarin samar da ayyuka gabanin zaɓen 2027 da kuma bayan kammala shi.
