Nijeriya a shekaru 66 : Wanne ƙalubale haɗin kan Nijeriya ke fuskanta?

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kowacce ranar ɗaya ga watan Oktoba tana zuwa wa ’yan Nijeriya a matsayin rana ta musamman, ranar nuna farinciki da jin daɗi, saboda murna da samun ’yancin kai da ƙasar ta samu daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila. Bayan gwagwarmaya da faɗi tashin da kakaninmu na baya suka yi wajen tabbatar da ganin al’ummar ƙasar nan sun samu ’yancin gudanar da mulkin kansu da tafiyar da harkokin siyasar ƙasarsu da kansu.

Ba za a ce an samu ’yancin cikin sauƙi ba, don mulkin mallaka, kamar yadda sunan ya nuna, mulki ne na nuna ƙarfin iko da zalunci da danniya. Ba ku da damar juya tattalin arzikinku da kanku, kuma komai naku sai kun nemi izini kafin a amince muku cikin sharuɗɗa masu tsauri. Ba ku da damar shiga takarar neman muƙamin siyasa ko riƙe wani matsayi na mulki, sai bisa tsarin da ‘yan mulkin mallaka suka yarje muku.

Nijeriya ta samu ’yancin kanta ne cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba, wannan ya nuna irin wayewa da kyakkyawan jagoranci da shugabannin gwagwarmayar neman ’yancin kai suka nuna a wancan lokacin. Shugabanni irin su Herbert Macaulay, Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe, Abubakar Tafawa ɓalewa, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin Nijeriya ta samu ’yancin kai daga turawan mulkin mallaka. Ta hanyar rubuce-rubuce a jaridu, da gwagwarmayar ƙungiyoyin ma’aikata, da na ’yan siyasa irinsu Akintola da Malam Aminu Kano. Haka nan marubuta da mawaƙa irinsu Malam Abubakar Imam da Malam Sa’adu Zungur, da Malam Abubakar Ladan Zariya, sun tayar wa da turawa hankali da irin basira da fasahohin da Allah ya basu. Wannan ya taimaka wajen samar wa ‘yan Nijeriya ’yancin kai a siyasance da harkokin tattalin arziƙi da zamantakewa.

Shekarar 1960 ta kasance shekarar da ƙasashen Afirka da dama suka samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka. ƙasashe irinsu Kamaru, Togo, Mali, Senegal, Iɓory Coast da Cadi, da suka karɓi ’yancin kansu daga turawan ƙasar Faransa. Da ƙasar Congo, Somaliya da Nijeriya, duk sun samu ’yancin kansu ne a shekarar 1960.

Samun ’yancin kai a wancan lokacin abu ne na farinciki ga ɗaukacin al’ummar ƙasar nan, duk da kasancewar ba kowa ne ya yi maraba da haɗin gambizar gabashi, kudanci, da arewaci da aka yi wa ƙasar da sunan haɗaɗɗiyar Nijeriya ba. Kuma a dalilin haka ne har kawo yanzu shekaru 66 da samun ’yancin kai ake cigaba da samun ƙalubale iri-iri, da ke barazana ga cigaba da kasancewar ƙasar a dunƙule a matsayin ƙasa ɗaya.

Tarihin Nijeriya ba zai manta da Yaƙin Basasa da ƙasar ta fuskanta ba a lokacin da ‘yan awaren yankin Biyafira, daga ɓangaren Kudu-Maso-Gabashin ƙasar nan, suka ayyana ɓallewa daga haɗin gambizar Nijeriya ba, wanda sanadiyyar haka aka samu asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi daga kowanne ɓangare, har ta kai ga dakarun gwamnatin Nijeriya suka samu galaba akan ’yan tawaye.

Haka kuma wannan matsala ta cigaba da tasowa lokaci zuwa lokaci, musamman daga yankin Inyamirai ’yan ƙabilar Ibo, da kuma yankin ƙabilar Yarabawa dake shiyyar yammacin ƙasa, inda aka samu wani ɗan kishin yarabanci Sunday Igboho da ya jagoranci wata ƙungiya mai ragin ware yankin Yarabawa daga Nijeriya, don kafa ƙasar su ta kansu.

A lokacin da Nijeriya ke ƙarƙashin mulkin mallaka, akwai ayyukan raya ƙasa, ingantattun hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, da masana’antu, da kuma kyakkyawan tsarin shugabanci da yake duba maslaha da jindaɗin talakawan ƙasa. Amma yanzu da aka samu damar faɗaɗa shugabanci da bunƙasar tattalin arziki, da ƙaruwar hanyoyin shigar kuɗaɗe, a maimakon a ga a cigaba da bunƙasa, sai abubuwa ne ke ƙara taɓarɓarewa, cin hanci da rashawa na ƙaruwa, shugabanni na cin amanar talakawa, ga zalunci da danniya a sha’anin mulki da rayuwa, wanda a kullum sai daɗa bayyana yake yi.

Musa Balarabe Musa, wani marubuci ɗan Nijeriya, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya bayyana cewa, ‘Dimukraɗiyyar da yanzu muke yi wacce ya kamata ta kawo wa talakawa sauyi mai ma’ana da ci gaban rayuwa ta zama makamin da ’yan siyasa ke amfani da ita wajen ƙara arzuta kansu da jefa talakawan ƙasa cikin yunwa da talauci.’

Wani marubucin tarihi, Basil Daɓidson, ya taɓa rubutawa cikin littafinsa mai taken, ‘The Struggle for Africa’s Independence’ cewa, ‘Samun ‘yancin kai bai taɓa zama cikar buri ba, sai dai ya zama masomin samun samun ingantacciyar rayuwa ga ‘yan ƙasa.’ Ya kamata ‘yancin kan Nijeriya ya zama ginshiƙin gina ingantacciyar ƙasa, bunƙasar tattalin arziki, samar da shugabanci nagari, da tabbatar da adalci ga kowa. Ba kamar yadda a yanzu muke gani yana faruwa, daga irin ’yan siyasa da ‘yan bokon da suke jagorancin ƙasar nan ba.

A yayin da Nijeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro da rigingimun ƙabilanci a tsakanin ’yan ƙasa, batun cigaba da kasancewar ƙasar a dunƙule na fuskantar babbar koma-baya. Kamar a baya da aka fuskanci matsalar ’yan aware ta Biyafira, wacce dakarun sojojin Nijeriya suka samu nasarar murƙushe ta, ’yan tada ƙayar baya masu ɗauke da makamai da sunan addini daga arewacin Nijeriya, da ake kira da Boko Haram, sun haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa, tare da haifar da rashin yarda da rabuwar kai a tsakanin ’yan ƙasar da ke bin koyarwar manyan addinan Musulunci da Kiristanci.

An samu gagarumar ɓaraka da rashin yarda wacce ta kai a duk inda aka ga ɗan Arewa a Kudu sai a riƙa ambatonsa da sunan Boko Haram. Har ta kai a wata jiha a Kudancin ƙasar nan an yi yunƙurin yi wa ýan Arewa katin shaida na musamman. Lamarin da ya nemi jefa ƙasar cikin wata mummunar damuwa. 

Bayan matsalar Boko Haram, Nijeriya ta sake samun kanta a wata matsalar tsaron wacce ita ma ta zo da nata ƙalubalen, musamman daga yankin tsakiyar Nijeriya. Matsalar tsagerun Fulani makiyaya masu ɗauke da makamai da ke rikici da manoma waɗanda akasarin su Kirista ne daga ƙananan ƙabilun tsakiyar Nijeriya, shima yana neman raba kan ƙasar ta fuskar addini. Ana zargin fitinar ’yan bindiga, ta hare-hare kan ƙauyuka, satar dukiyoyi da garkuwa da mutane, wani yunƙuri ne na mamaye yankin, don canza musu addini ko ƙwace musu ƙasa da sunan addini da ƙabilanci. 

Duk da kasancewar waɗannan zarge-zarge ne marasa tushe, amma haɗin gambizar ƙabilu da auren dole tsakanin shiyyoyin ƙasar nan na cigaba da zama barazana ga cigaba da haɗin kan ƙasar nan. ɓangarori da dama na ganin ba a yi musu adalci, ko kuma ba a rabon muƙamai ko arziƙin ƙasa da su yadda ya dace. Yayin da ’yan Arewa ke zargin ƙarfin manyan ayyukan gwamnati da yawan ɗaukar ma’aikata a aiki, ya fi karkata a yankin Kudu. Akasari kuma jihohin Arewa sai fama da yunwa da talauci da rashin kulawar gwamnati, ga kuma yawan matasa masu zaman banza ba aiki. 

Lallai akwai buƙatar gwamnati da duk masu faɗa a ji na ƙasar nan su tabbatar da an yi wa kowanne yanki adalci, bare da nuna fifikon wani sashi ba. A tabbatar da an inganta tsaro da zaman lafiya a dukkan yankunan ƙasar, ba tare da an cutar da wasu saboda raunin da suke da shi ba. Kada shugabanni su bar wata ƙofa da wani zai yi tunanin gara ma ya balle daga ƙasar zai fi masa cigaba. 

A yayin da nake taya ɗaukacin ’yan Nijeriya murna da zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai, ina kira a gare mu bakiɗaya mu haɗa kai mu rungumi juna a matsayin mu na ’yan Nijeriya. Mu daina bari bambance-bambancen addini da ƙabilanci su cigaba da kawo ɓaraka a tsakanin mu.

By ukarofi

Leave a Reply