2027: Babu gurbin ‘yan adawa a gidan gwamnatin Zamfara – Namadi Kasuwar Daji

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara na musamman kan harkokin siyasa, Hon. Namadi Isah Kasuwar Daji, ya bayyana cewa babu gurbi ga jam’iyyun adawa a gidan gwamnatin Jihar Zamfara a zaɓen 2027.

Hon. Kasuwar Daji ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau ranar Laraba.

A cewarsa, ‘yan adawa irin su Sanata Kabir Garba Marafa da Hon. Bilyaminu Yusuf Shinkafi na NDC da ADC ba su da wani sabon abu da za su bayyana wa al’ummar Jihar Zamfara a lokacin yaƙin neman zaɓen da ke tafe.

“A 2027, jam’iyyun adawa musamman NDC da ADC ba barazana ba ne ga APC a Jihar Zamfara. muna da abubuwa masu yawa na zahiri da za mu nuna a fagen ci gaban ababen more rayuwa yayin kamfen ɗin mu,” in ji shi.

Hon. Namadi Isah Wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal ya cimma manyan nasarori a fannoni daban-daban na tattalin arziki a cikin shekaru uku na mulkinsa ƙarƙashin ajandar sa ta ceton jihar.

“Dimokuraɗiyya tana nufin abin da ka shuka a rayuwar al’ummarka wanda ya shafe su kai tsaye, ba farfaganda a siyasa ba,” in ji shi.

Ya ƙalubalanci cewa babu wani ɗan siyasa a Jihar Zamfara da zai iya fafatawa da gwamna Dauda Lawal a babban zaɓe mai zuwa idan aka duba ayyukan raya ƙasa da ya yi.

“Babu wani ɗan takara da zai iya fafatawa da Gwamna Dauda Lawal a zaɓe mai zuwa idan aka yi la’akari da ci gaban ababen more rayuwa da ya yi a ƙarƙashin ajandar cetonsa a cikin shekaru uku da suka gabata,” in ji shi.

Hon. Namadi Isah ya nuna ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓe tun daga sama har ƙasa, ba a Jihar Zamfara kaɗai ba har ma da ƙasar baki ɗaya a babban zaɓen 2027.

Haka zalika ya yi kira ga mambobin jam’iyyar APC da magoya bayan ta da su kasance masu bin doka da oda tare da haɗa kai don samun nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a zaɓen da ke tafe.

By ukarofi

Leave a Reply