
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ‘yan Nijeriya za su fara siyan fetur a farashi mai rahusa a gidajen man NNPCL har na tsawon wata guda.
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattali, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.
Ya ce, za a samu ragi a kowace lita daga ainihin yadda aka saba siya. A cewarsa gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne da nufin samar da sauƙi ga al’umma musamman bisa la’akari da masu harkar sufuri na ‘yan kasuwa.
Sannan, ya ce gwamnatin tarayyar za ta kafa tsarin da zai bayar da yanayin samar da rangwamen farashi da za a riƙa sabuntawa a kowane wata.
