
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Alhaji Yayale Ahmed, yaba wa Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf kan nasarorin da hukumar ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa, inda ya ce ana samun kyawawan sakamako a harkokin jigilar alhazan Nijeriya.
Yayale Ahmed, wanda kuma shi ne Ajiyan Katagum, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara a babban ofishin NAHCON da ke Abuja.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’ar hukumar, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar, ya ce a yayin ziyarar, tsohon sakataren gwamnatin ya kuma bayar da shawarwari na dabarun da za su taimaka wa jagorancin NAHCON wajen inganta harkokin gudanarwa da jigilar alhazan Nijeriya.
Ya ce, babban baƙon ya kuma bayyana gamsuwarsa bisa nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Ambasada Yusuf musamman wajen fifita walwalar alhazai, yana mai kira da a yi ƙoƙarin ɗorewa akan hakan.
A nasa jawabin, Shugaban na NAHCON, Ambasada Yusuf ya bayyana Yayale Ahmed a matsayin muhimmin mai ruwa da tsaki, wanda ƙwarewa a harkokin gudanarwa da hangen nesansa za su cigaba da kasancewa ababen da ake buƙata a harkokin hajjin Nijeriya. Ya kuma yi godiya a gare shi kan ziyarar da kuma fatan cigaba da samun shawarwari da ra’ayoyinsa akan lamuran NAHCON da walwalar alhazan Nijeriya.
Kazalika, ambasadan ya tabbatar masa da cewa NAHCON za ta cigaba da nuna kwaɗayinta akan karɓar hikimomin muhimman masu ruwa da tsaki irinsa yayin da take ƙoƙarin aiwatar da matakai da manufofin samar da gyare-gyaren ayyukanta domin sauke nauye-nauyen da ke kanta bisa inganci.
