Kotu ta kori ƙorafin El-Rufa’i na neman haramta wa EFCC da ICPC kama kadarorinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta yi watsi da ƙorafin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shigar a gabanta na neman ta katange Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da wasu hukumomin kula da biyayya ga doka daga sanya wa asusun bankunansa takunkumi ko ƙwace kadarorinsa.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yi hukuncin a ranar Alhamis bayan ta ce ƙorafin cin fuska ne ga matakan kotu. El-Rufa’i dai ya shigar da ƙorafin ne akan ICPC, EFCC, DSS da Antoni Janar na Ƙasa (AGF) a matsayin waɗanda ake ƙara na ɗaya zuwa na huɗu.

A yayin hukuncinta, Alƙali Joyce ta amince da amsar waɗanda ake ƙara cewa tsohon gwamnan ya shigar da irin ƙarar a Babbar Kotun Abuja da Babbar Kotun Tarayya, inda ta ce ba zai yiwu a yi amfani da kotu wajen hana biyayya ga hukunce-hukuncen doka ba akan hukumomin da aka ɗora wa alhakin kula da lamuran, don haka ne ta yi watsi da ƙorafin bisa abin da ta kira da zargi da rashin nagarta.

Haka kuma, mai shari’ar ta ce matakin bai bayyana dalilin da zai sa a ɗauki matakin hukunta EFCC, DSS da AGF ba don haka ta cire sunayensu a matsayin waɗanda ake ƙara. Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Oluwole Iyamu ne ya shigar da wannan ƙorafi a takarda mai lamba FHC/ABJ/CS/368/2026, wadda aka shigar tun a ranar 24 ga Fabarairu, 2026.

Tsohon gwamnan dai ya nemi a haramta wa ɓangarorin ɗaukar matakan sanya takunkumi ga asusun bakunansa ko karɓe iko da kadarorinsa ne har zuwa lokacin da za a kammala shari’arsa. Ya kuma buƙaci kotun ta ayyana cewa baki ɗaya kadarorinsa mallakinsa ne da ya same su ta halastattun hanyoyi. Sannan, ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan ɗaya kan tauye masa ‘yanci yayin bin hanyoyin gurfanar da shi daga ɓangaren hukumomin.

Saidai, ɓangarorin sun musanta dukkan abin da tsohon gwamnan yake tuhumar su a kansu tare da kira ga kotun da ta yi watsi da buƙatun da ya gabatar mata na ɗaukar mataki akansu.

By Babaji

Leave a Reply