Daga AISHA ASAS
Fitaccen jarumin Bollywood, Amitabh Bachchan, ya sake ɗaukar hankalin masoyan fina-finan Indiya bayan wani yanayi na ban dariya da ya faru tsakaninsa da jarumar Bollywood, Madhuri Diɗit, a shirin Kaun Banega Crorepati (KBC) na kakar 18.
A wani shiri na musamman, Bachchan ya tuna yadda ya taɓa kwaikwayon wani salon rawa da Madhuri ta yi a fim ɗinta na ‘Tezaab’, inda ya yi amfani da salon daga waƙar “Ek Do Teen”. Daga baya ya nemi gafararta a bainar jama’a, yana mai cewa ya yi “babban kuskure”.
Sai dai lamarin bai kasance wata rigima ba, domin komai ya gudana ne cikin raha da girmamawa tsakanin manyan jaruman biyu. Madhuri, wadda ta kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman da Bollywood ta samar, ta kuma fito da wani ɓangare na rawar da ta shahara da ita a Devdas, abin da ya sa Bachchan da sauran waɗanda ke wajen suka yaba mata.
Madhuri ta kuma halarci wani shiri na musamman da aka shirya domin bikin cikar Bachchan shekara 84, inda ɗansa, Abhishek Bachchan, ya bayyana a dandalin shirin ya kuma rungumi mahaifinsa. Wannan shiri na musamman ne ake sa ran za a watsa ranar 9 ga Oktoba.
