‘Yan sanda sun tare hanyar zuwa wajen taron TMG a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu daga cikin mambobin tafiyar ‘Tinubu Must Go’ (TMG) sun koka bisa zargin tare musu ƙofar shiga wajen da suka tsara gudanar da taronsu a Jihar Kano, inda suka zargi jami’an hukumar ‘yan sanda da hana su aiwatar da abin da dokar ƙasa ta ba su dama.

Lauya Abba Hikima, wanda ɗaya ne daga cikin jagororin tafiyar, ya bayyana damuwarsa akan al’amarin, inda ya zargi ‘yan sanda da hana mambobinsu shiga gurin taron da suka biya kuɗi domin su yi harkokinsu.

Wannan tafiya ta bayyana kanta a matsayin wadda ba ta da jam’iyya guda da take alaƙanta kanta da ita, saidai tana kira zuwa ga wayar da kan jama’a musamman ‘yan Nijeriya wajen kayar da Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Da yake jawabi a wani faifan bidiyo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook, Abba Hikima ya yi zargin cewa motocin ‘yan sandan mobail guda 10 ne aka jibge a wajen da suka shirya gudanar da zaman nasu. Kuma An hango wasu jami’an tsaro acikin bidiyon. “Ta bayyana a fili ga ‘yan Nijeriya cewa Tinubu ya gaza. Ta bayyana ga dukkan ‘yan Nijeriya cewa Tinubu ya gaza kuma akwai buƙatar ‘yan Nijeriya su fito su kayar da shi,” inji Abba Hikima.

Lauyan ya kuma koka musamman akan yadda suka biya kuɗi domin gudanar da taron kamar yadda suka tsara, amma aka hana su, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa dokar ƙasa da ta ba su ‘yancin bayyana ra’ayi, yana mai cewa “Wannan ma kaɗai dalili ne da ya sa Tinubu sai ya tafi”.

Ya kuma yi iƙirarin shaida wa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori batun taron, inda ya ce masa za su gudanar da shi cikin lumana tare da kiyaye doka da oda, sannan ya ƙara da cewa doka ma ba ta hukunta sai an nemi izinin ‘yan sanda kafin a yi irin wannan taro ba.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, hukumar ‘yan sanda ba ta fitar da saƙo ba kan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply