Ministan Labarai ya jinjina wa salon yaƙin neman zaɓen APC a Arewa ta Tsakiya, ya buƙaci a karkata ga masalahar al’umma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, ya yaba wa dunƙulewa da goyon baya da aka nuna yayin buɗe yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki (APC) a Arewa maso Tsakiyan Nijeriya, wanda aka gudanar a garin Lafian Jihar Nasarawa, inda ya yi kira ga jiga-jigan siyasa da su fifita zaman lafiya da muhimman al’amuran ƙasa aciki yayin tunkarar babban zaɓen 2027.

A cewar wata sanarwa ta ranar Lahadi da Mai taimaka wa ministan kan Harkar Labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar, Mohammed Idris ya ce gangamin ya bayar da damar isar da saƙon Gwamnatin Tarayya na fifita ayyukan ci-gaba, ciki har da tsaron abinci, da damawa da kowane ɓangare a shugabanci, yana mai cewa ya dace a ce yaƙin neman zaɓen ya karkata ga tsare-tsare, ayyukan da aka aiwatar da ƙoƙarin da ake yi wa ‘yan Nijeriya a madadin rikici ko cacar baki.

“Idan kana da abin siyarwa, ba ka da buƙatar yin faɗa. Mu na da abin siyarwa ga Nijeriya, kuma shi ya sa muke gudanar da wannan taro domin nuna wa ‘yan Nijeriya abin da muka tsaya wa,” inji Ministan.

A nasa kalaman, Ƙaramin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu S. Abdullahi ya bayyana muhimmancin cigaba da bayar da kula da tsaron abinci da inganci lamuran sufuri wajen rage tsadar kayan abinci a kasuwanni. Ya ce, “Duk da ƙalubalen, za ku ga an samu ɗorewa a tsarin abincinmu, kuma muna aiki tuƙuru don ganin hakan ya cigaba da ɗorewa.”

Ita ma a nata jawabin, Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, ta ce mata, yara da marasa galihu suna da muhimmanci ga ajandar ci-gaban ƙasa, domin an tsara shirye-shiryen gwamnati ne don warware matsalolin buƙatunsu na yau da kullum.

By Babaji

Leave a Reply