Daga MUHAMMAD SANI CHINADE a Damaturu
Hukumar hisbah ta Jihar Yobe ta kama mata shida da ake zargi da yin aikin karuwanci a lokacin wani samame da suka kai a garin Gadaka cikin ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe.
Jami’an hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar Fika ne suka gudanar da aikin a yankin unguwar Abuja da ke garin Gadaka.
Shugaban gudanarwa na hukumar a ƙaramar hukumar Fika, Malam Musa Abari Talba, ya shaida wa manema labarai cewa jami’an hukumar ne suka gudanar da aikin a ƙarshen mako.
A cewar rahoton wannan samame bai tsaya ga haka ba, sun kuma kai ƙarin samame a wurin da ake sayar da barasa.
A cewarsa, jami’an na hisbah sun gudanar da gangamin wayar da kan jama’a kuma sun gargaɗi mazauna yankin game da ayyukan da suka bayyana a matsayin waɗanda suka saɓa wa ƙa’idojin addini da zamantakewa.
Ya ƙara da cewa jami’an sun yi wa mazauna yankin wa’azi kuma sun buƙaci su bi doka da oda tare da guje wa ayyukan da ake ganin suna cutar da ɗabi’un al’umma.
Talba ya ce aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar na inganta zaman lafiya, ɗa’a da kuma kyawawan halaye a tsakanin mazauna jihar.
Ya ƙara da cewa za a ci gaba da irin wannan aiki a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da bin doka da kuma haɓaka rayuwar al’ummomi faɗin jihar Yobe.
