
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ankarar da ‘yan Nijeriya kan wata wallafa ta yanar gizo da ta shafi jaddawalin ‘yan takarar gwamna a jihohi guda shida, tana mai gargaɗi akan yaɗa labarai masu ruɗarwa akan zaɓe.
INEC ta zayyano jihohin Zamfara, Gombe, Delta, Filato, Yobe da Kano a matsayin waɗanda al’amarin ya shafa, tana mai bayyana hakan a matsayin damfara. Don haka ta shelanta wa jama’a cewa wallafar ‘yar jabu ce kuma saƙon ciki ba daga gare ta ya fito ba.
Hukumar zaɓen ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da shi da kuma ƙaurace wa cigaba da yaɗawa, inda ta kuma yi gargaɗin hakan abu ne da zai iya ruɗar da jama’a.
Kazalika, ta ce ba ta fitar da wani saƙo na musamman ba akan ‘yan takarar gwamna a jihohi shidan da ta lissafo don haka kada jama’a su ruɗu da shi.
Sannan, ta shawarci al’umma da su riƙa ziyartar sahihin shafinta na yanar gizo don samun sahihan bayanai (inecnigeria.org), tana mai jaddada aniyarta ta samar da ingantattun labarai akan ababen da suka shafi harkokinta.
