Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
In ba addini da ƙabilarsu ta gaskiya zallawa ke ɓoyewa ba, mai ya sa su ke ɓoye ruff a salula ba hoto ba sunan gaskiya? in ka ga bazalle ya wurgo ashar za ka taras shafinsa a rufe ne ruff don makirci da annamimanci.
Wallahi mafi rinjayen ‘yan kwangilar Zallawa na AIFOB da Midibelawa da ke zagin malaman Musulunci a boye su ke ruff a wayar salula ba sunan gaskiya, ba hoto kuma ba ma adireshi sai zayyanar Sarkin busa da wasu hotunan bogi na nuna rubuce-rubuce tamkar kasar Hausa da wasu masu rawunna alhali masu saka hotunan ko da wasa ka gansu ma’abota hana-sallah ne maƙiya hulunan gaskiya balle har a je ga rawani!.
Zallawa kan ce su ‘yan gwagwarmaya ne amma kullum sai kara buya su ke yi. Shin sun zama ‘yan gwagwarmaya ko ‘yan gararamba? Duk wanda za ka ga ya mulmulo zagi mai maiko ya zagi manyan malaman musulmi sai ka taras shafinsa a rufe ruff don ya tabbatar shi kansa na bogi ne kuma annamimi. Su kan ce wai su na buya ne don kar a kai mu su hari. Shin waɗanda a ke kai wa hari a ƙauyuka ba sa ɓoye kansu a soshiyal midiya ne ya jawo mu su haka?
Tabbas mutanen nan na buya ne don su na son su yi shigar burtu a matsayin Musulmi alhali ba Musulmi ba ne kazalika don a ɗauka Hausawa ne alhali Midibelawa ne da Maguzawa da dama asalinsu wasu ƙabilu ne da su ka narke su ka zama masu magana da harshen Hausa amma su na da yarukansu da su ka bace bat. Ku dubi waɗanda su ka bayyana ‘yan ƙalilan tsaf za ku ga ba su yi kama da Hausawa daga ma zubin fuskarsu, kai balle su ka yi magana za ka ji tsamin baki na gwaranci kamar mai son cewa TSALLE sai ya ce SALLE ko NAJERIYA sai ya murguda baki ya ce NIJEIRIYA ko kunya ba ya ji don mai yaudara ne. Ko wani daga madugunsu haka harshensa ya ke a nannade kamar curin ulu gabanin a watsa a algasa ko zaren kunkumadi kafin warewa a ɗinka hula.
Ina kira ga duk al’ummar Arewa a zauna lafiya, Musulmi ya yi addininsa hakanan Kirista ma ya yi na sa a guji shigar burtu kan kwangilar Midibelawa da AIFOB. In Arewa ta samu matsala to ba shakka Midibelawa ba su da asara balle AIFOB. Duk wake-wake da ke garuruwan kokuwar Arewa su fito a wake garas, Hausa-Kiristan su yi ibadarsu ba wanda ya hana su haka nan musulmi su yi nasu kamar yadda tsarin mulki ya ba da hurumi. Hatsari ne kwarai zagin shugabannin wani addini ta hanyar fakewa da wai kwato haƙƙin Hausawa. Shin waye Bahaushe a wajen Bazalle? Bahaushe a wajen Bazalle shi ne mai Zunduma ashar ga Shehu Mujaddadi, barazanar aukawa fadar sarakunan Arewa da zagin Musulmi a kaikace alhali duk wanda ba Musulmi ba ko yaron Turji ne ya tsira.
Wallahi na taɓa gamuwa da Bazalle mai mugun nufi a haramin makkah amma ba alamar aikin hajji ya yi. Shaida na tabbata ta tura wasu zallawa masihiyya ƙasashen Larabawa su koyo larabci da zummar dagula Musulunci
Kamar yadda na yi ƙalubale ga Zallawa da nuna ko mutum daya tak wanda ba musulmi ba da su ka taba zagi tatas ta uwa ta uba amma sai tsit ba amsa, mutanen na cigaba da shigar burtu inda za ka ga ɓoyayyen mutum ruff a salula ya rubuta “ni Bahaushe ne Musulmi…” shin tsakani da Allah Bahaushe na buƙatar sai ya ce ma ka shi musulmi ne? A nan na ke kara shawartar Hausa-Kiristan da ba su shiga barandar AIFOB da Midibelawa ba su yi takatsantsan don duk wanda ya gina ramin mugunta shi zai iya ruftawa ciki kuma ba wani dan AIFOB da zai kawo ma sa ɗauki tun da shi ABOKI ne.
Akwai wasu Hausa-Kiristan da a yanzu ke wa’azinsu da jan ayoyin Alkur’ani su na fassarar gatari. Duk ba ma wadannan ne babban hatsari ba, sai wasu ‘yan mishan masu iƙirarin Hausa da kan nuna su malaman musulunci ne alhali ba sa saka kowane littafi su karantar sai kokarin jayayya da mara baya ga ƙabilanci wai kishin ƙabila ne sai kuma gutsoro wasu sassan littattafan Shehu Mujaddadi don cin mutunci da shirga sharri. Kifi na ganinka mai jar koma. Yaya za a yi malamin musulunci na gaskiya zai koma zafafa ƙabilanci da neman a shiga yaƙi? Akwai wasu da ke da ‘yan uwa Maguzawa don haka shaidan ya kawata mu su kare muradun ‘yan uwansu da fakewa da inuwar Musulunci.
Haƙiƙa na taba gamuwa da wani Bazalle mai mugun nufi a haramin Makkah kuma gaskiya ban ga alamar ruhin ibadar hajji a jikinsa ba ta yiwu ya je yawon bude ido ne ko sanin sirrin musulmi. Na ga wani ma mai yayata harkar mishan na cewa an ba shi kujerar Makkah daga wai wani mutumin kudu wanda ba mamaki na daukar duk wani ABOKI a matsayin Musulmi. Bazallen dai bai ce zai je hajjin ba don haka ba mamaki in labarin ma gaskiya ne ya sayar da kujerar ya zura canjinsa a ramin tela. Allah suturi bukui.
Muhimman ƙalubale ga Zallawa biyu ne kacal:
1. Su ambata mutum daya tak shahararre wanda ba Musulmi ba da su ka taba yi wa wankin babban bargo. Hatta Fulanin da su ke adawa da su a Filato ba sa hadawa da Fulani-Kiristan!
2. Duk su bayyana daga ɓoye kansu ruff a salula da su ka yi. Su fito da sunayensu na gaskiya, hoto da adireshi da ma addini tun da sun ce da ɗan tauhidi da dan mishan duk sammakal ne a wajensu. Mu ga sun matsawa boyayyu lamba da su bayyana. Shin wannan buya ba shaida ce ta makirci da annamimanci ba? Shin hakan ba alamun mugayen mutane ne masu kulle-kullen aikata miyagun laifuka na ta’addanci ko tunzura wasu su shiga ɗauki ba daɗi da juna a doron ƙabilanci ba? Ai gaskiya ta bayyana ƙarara kamar hasken rana da 12pm.
Zallawa na neman bata sunan dan takarar jam’iyyar accord Gbenga Olawepo Hashim da bugin ƙirji wai dantakararsu ne! ra’ayin Hashim ya yi nesa da farafagandar Zallawa ta ruruta fitinar kabilanci don ya karanto baibul sura ta 17 aya ta 24-26 a littafin Ayyukan Manzanni
Ya zama wajibi duk ‘yan takarar kujerun siyasa da ke son bin doka da neman ƙuri’ar Arewa su nesanta kan su da Zallawa don ‘yan farafaganda ne kawai a soshiyal midiya da fakewa da karyar kare Hausawa don biyan muradun kashin kai na son zuciya. An wayi gari kawai na ga su na yayata hotunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ACCORD Gbenga Olawepo Hashim wai a matsayin dantakararsu wai zai kare muradunsu! Duk wanda ya ce zai kare muradun Zallawa to Wallahi makiyin Arewa ne na bugawa a shafin farko na jarida. Ba inda na ga Hashim ya ware Zallawa ko wasu gungun mutane ya ce su ne nasa hasalima shi ya na nuna duk al’ummar Nijeriya ɗaya ne kuma nasa ne.
Gbenga Hashim wanda a ka haifa a Kebbi a 1969 bai samu zama na morewa da mahaifinsa CP Hashim Abdullahi ba lokacin ya na yaro don ya girma ne a wajen mijin mahaifiyarsa Mr.Julius Bamidele Olawepo a New Bussa jihar Neja. Ya bayyana tarihin shan wuya da ya yi don hatta lokacin ya na makarantar kwana ba a kai ma sa ziyara kamar sauran ɗalibai kuma don yanayin rashin kyawun kayansa har wani mai koyar da wasan kwallon hannu na tsangwamarsa inda ya kan koma bayan fage ya fashe da kuka. Sai dai ya ce kukan bai shafi tunaninsa na samun nasara a rayuwa ba tun da har Burtaniya ya samu zuwa karatu.
Gbenga ya harhaɗa sunan mijin mahaifiyarsa “OLAWEPO” da na asalin mahaifinsa “HASHIM” ya tada sunan Gbenga Olawepo Hashim. Da alamu wasu mutanensa ba su ji daɗin yadda ya ƙara HASHIM mai alamar Musulunci da kuma Hausa ba a cikin sunansa. A wata zantawa Gbenga ya ja Sura ta 17 aya ta 24-26 a Ayyukan Manzanni cikin Baibul inda a ke bayanin Allah ne mai kowa kuma duk mutane ‘yan uwan juna ne wato jini daya ne ba ZALLANCI balle BAZALLE! Hakanan Gbenga ya ce ba mamayar wata ƙabila a waje ɗaya ko ƙabilanci ne ke kawo nasara ba amma samun jagoranci nagari ya na mai buga misali da Sudan ta kudu wacce jama’arta su ka nace sai sun balle bayan kimanin shekaru 30 a na gwabza yaƙi a Sudan amma bayan samun nasara sai ya zama aikin baban giwa don fitinar ko kusa ba ta kare ba.
Don wata tawagar Zallawa ta gana da Hashim a Abuja ya ba su kuɗin jirgi da tura kyautar Naira miliyan 2 ga wata mai bin muradunsu, ba shi ke nuna Gbenga a matsayin ɗan takarar Zallawa ba. Siyasa ta wuce wani ko wata ‘yar ƙungiya mai ruruta fitinar ƙabilanci ya ko ta danganta kanta da wani ɗan takara. Duk bayanan da mu ka gani na Gbenga na hannun riga da muradun Zallawa. Ko Gbenga ya yi tasiri a zaben ba don farafagandar Zallawa ba ne.
KAMMALAWA
Na ga wasu kuma na wurgo wani hoto na Hashim da Janar Babangida. Ba don kar ya zama ƙauyanci ba da ni ma na wurgo hotuna na da Janar ɗin mu ga ta farafaganda. Ai shi Janar uba ne ga kasa kuma duk ‘yan takara ka iya kai ma sa ziyara ya dau hoto da su.
ƙALUBALE-Zallawa su fito da faifan bidiyo ko ma sauti na Gbenga Olawepo inda ya ce shi ɗan takararsu ne ko ya yarda su zama sojojin kamfen ɗinsa a Arewa.
