Tsofaffin sojoji sun tare mashigar hukumar fansho a Abuja kan rashin biyan haƙƙoƙinsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata tsofaffin jami’an sojoji suka yi dandazo a mashigar Hukumar Fanshon Sojoji da ke yankin Kubwa a Abuja, inda suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa ga gyare-gyaren da aka yi wa tsarin fanshonsu tare da zargin rashin biyayya ga biyan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi.

An ga yadda tsofaffin sojojin suka tare mashigar ofishin da tantina da kujeru tun da misalin ƙarfe 8 na safe, suna nuna rashin gamsuwa da aiwatar da gyare-gyaren, yayin da sojoji suka hana su shiga cikin farfajiyar ofishin.

Wannan na zuwa ne makonni bayan sojojin da suka yi ritaya sun yi gangami a ofishin Ma’aikatar Tsaro a watan Satumba, inda suka nemi a yi ƙarin kuɗaɗen fansho da ake biyan su bayan an yi wa jami’an da ke bakin aiki ƙarin albashi.

Kodinetan tsofaffin dakarun, Laftanal Kanal Innocent Azubike, ya zarg hukumar da bin tsarin fansho da ake zargin ya rage kuɗaɗen wasu tsofaffin jami’ai, yana mai cewa hakan ya haifar da rashin daidaito a matakan biya daban-daban na masu ritayar.

Kazalika, ya koka kan abin da ya kira da gazawar hukumar ta warware matsalolin ƙorafe-ƙorafensu, inda ya yi zargin cewa wannan sauyi da aka samu a tsarin biyan su fansho ya haifar da fushi acikin tsofaffin sojoji.

Wannan al’amari dai ya nuna yadda rikici tsakanin jami’an da mahukunta ya yi ƙamari kan haƙƙoƙinsu na fansho, biyo bayan bore da suka yi a Ma’aikatar Tsaro a Satumba.

By Babaji

Leave a Reply