Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Hukumar Ilimi ta bai ɗaya ta Jihar Zamfara (ZSUBEB), tare da haɗin gwiwa hukumar ilimi ta bai ɗaya ta ƙasa (UBEC), ta ƙaddamar da shirin horarwa na kwanaki huɗu kan haɗa fasahar ICT da koyarwa domin ƙarfafa koyo da koyarwa ta hanyar fasaha a makarantun bai ɗaya na jihar.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ibrahim Musa Maizare ya fitar, shirin an tsara shi ne domin bai wa ma’aikatan ilimi da ƙwarewa ta zahiri kan yadda za su haɗa fasahar sadarwa ta zamani (ICT) cikin koyarwa da koyo a aji.
Sanarwar ta bayyana cewa horon ya haɗa mahalarta 65, waɗanda suka haɗa da jami’an ICT na Jiha 10, Malaman ICT 50, da Jami’an LGEA Desk Officers guda biyar daga sassan jihar.
Ana sa ran mahalartan za su samu ƙwarewa da za ta taimaka wajen tallafawa koyon na’ura mai kwakwalwa da inganta yadda ake bayar da darussa a makarantun bai ɗaya.
Da yake jawabi a wajen buɗe taron, shugaban zartarwa na hukumar, wanda daraktan data, digital platform and analytics (DDPA), Dalhatu Muhammad Jangebe ya wakilta, ya jaddada buƙatar samar da kayayyakin na’ura mai kwakwalwa kawai zuwa tabbatar da amfani da su yadda ya kamata a ajujuwa.
Ya bayyana cewa fasaha ya kamata ta zama kayan aiki mai matuƙar amfani wajen sanya darussa su zama masu jan hankali, mu’amala da inganci, ta yadda za ta inganta shiga, fahimta da ƙwazon ɗalibai a karatu.
Jangebe ya bayyana cewa horon ya ƙunshi muhimman fannoni kamar tsara darussa ta hanyar fasaha, ƙirƙirar kayan koyarwa na zamani, sarrafa ƙarancin kayan koyarwa, da dabaru na yadda ake raba na’urori yadda ya kamata.
Ya ce an mayar da hankali ne domin taimakawa mahalarta su yi amfani da kayayyakin ICT da ake da su da kuma ƙarfafa amfani da fasaha wajen koyarwa da koyo, musamman a makarantun da ke da ƙarancin kayayyaki.
Ya ƙarfafa wa mahalarta horon ƙwarin gwiwar su yi amfani da wannan horo, su raba ƙwarewa tare da aiwatar da ilimin da suka samu a wuraren aikinsu.
Ya kuma buƙace su da su zama jakadu wajen tallafawa sauran malamai wajen amfani da hanyoyin koyarwa da ke da taimakon fasaha domin inganta tsarin ilimin bai ɗaya a jihar.
Hukumar ta gode da ci gaba da goyon bayan da UBEC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi ke bayarwa wajen ƙarfafa sauyi na zamani da bunƙasa karfin ma’aikatan ilimi a fannin ilimi bai ɗaya, tare da yabawa masu horarwa kan ƙudirinsu na ƙarfafa haɗa ICT cikin makarantu.
Horon na kwanaki huɗu, wanda ya fara ranar Litinin, 13 ga Oktoba, 2026, zai kare ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026.
Wannan shiri, a cewar hukumar ta ZSUBEB, wani ɓangare ne na ci gaba da kokarinta ƙarƙashin jagorancin Farfesa Nasir Garba Anka na inganta ƙa’idojin koyarwa, ƙarfafa ƙarfin ma’aikatan ilimi, da ƙarfafa sabbin hanyoyin koyo a faɗin Jihar Zamfara.
