
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Jihar Legas, ta samar da tsarin lambobi na Quick Response (QR) domin taimaka wa masu zaɓe gano cibiyoyin karɓar katin zaɓensu (PVC) gabanin babban zaɓen 2027, yayin da hukumar ta kuma sanar da sababbin lokutan zaɓe bayan sauya fasalin dokar zaɓe.
INEC ta ce, za ta wallafa lambobin na QR a shafukanta na sada zumunta da sahihin shafinta na yanar gizo domin bai wa masu zaɓe damar gano inda za su karɓi katinsu cikin sauƙi yayin da babban 2027 ke cigaba da ƙaratowa.
Kwamishinan zaɓen Legas, Farfesa Ayobami Salami yayin ganawa da manema labarai a Legas, ya yi kira ga al’umma da su karɓi PVCs ɗinsu ta sahihan hanyoyin da INEC ta amince da su, wanda zai ba su damar tantance halin rajistarsu yayin da hukumar ke faɗaɗa shirye-shiryen zaɓukan.
Da fari, INEC ta ayyana Asabar, 20 Fabarairu, 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasa, yayin da ta sanya na gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi a Asabar, 6 ga Maris, 2027 bisa biyayya ga Dokar Zaɓe ta 2022.
Saidai bayan sake nazari kan dokar da ƙoƙarin aiwatar da Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ta samar da damarmakin gyare-gyare ga lokutan jagorancin gabanin zaɓe da lamuran zaɓe, hukumar ta sake nazari tare da ƙoƙarin daidaita tsare-tsarenta domin tabbatar da cikakkiyar biyayya ga sabon tsarin dokar.
Akan haka ne ta sanar da cewa a yanzu an mayar da na shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa ranar Asabar, 16 ga Junairu, 2027, yayin da za a yi na gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi a ranar Asabar 6 ga Fabarairu, 2027.
