Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ma’aikatar lafiya ta Jihar Nasarawa, tare da haɗin gwiwar asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lafia, ta shiga sahun sauran ƙasashen duniya wajen gudanar da bikin ranar lafiyar ƙwakwalwa ta duniya na bana tare da tafiyar faɗakarwa da nufin jawo hankali kan halin da mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa ke ciki.
Tafiyar, wadda aka gudanar a Lafia, ta samu jagorancin wani ƙwararren likitan taɓin hankali na asibitin, Dakta Paul Agbo.
Da yake zantawa da manema labarai yayin gudanar da aikin, Dakta Agbo yace tattakin na daga cikin ayyukan da aka tsara domin bikin ranar, wadda ake gudanarwa a duniya a kowace 10 ga watan Oktoba.
A cewarsa, an ɗage bikin na bana ne saboda ranar 10 ga Oktoba ta faɗo a ranar Asabar.
“Yau muna gudanar da bikin Ranar Lafiyar Kwakwalwa ta Duniya tare da tafiya. A saba, ana gudanar da ita a kowace 10 ga Oktoba, amma 10 ga Oktoba ya fado ranar Asabar, don haka muka yanke shawarar yin tafiyar yau,” in ji shi.
Dakta Agbo ya bayyana cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta keɓe wannan rana ne domin mayar da hankali kan buƙatu na musamman na mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, wadanda galibi ke fuskantar kyama da nuna wariya.
“Ranar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ana bikin ta ne a kowace 10 ga Oktoba a kowace shekara. Kuma ainihin manufarta ita ce jawo hankalin duniya kan abubuwan da suka shafi lafiyar ƙwakwalwa. Mutane masu fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa rukuni ne na musamman. Sun fi fuskantar kyama,” in ji shi.
“Don haka WHO ta yanke shawarar cewa ya dace a kebe rana domin girmama su, domin a fito da tunani, da abubuwan da suka kebanta da su, da buƙatunsu, da kuma musamman ainihin ɗan Adam — saboda su ma mutane ne. Don haka wannan rana ce da WHO ta keɓe domin mu murnar buƙatu da burin musamman na waɗanda matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa suka shafa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa taken bana shi ne, “Abubuwan da aka fuskanta, Lafiya, Murya ta Gaskiya, da Sauye-sauye na Gaskiya,” wanda ke neman ba da murya ga mutanen da suka fuskanci taɓin hankali da idanunsu.
“Manufar ita ce mu ji daga bakin mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, jami’in kula da lafiyar ƙwakwalwa na ma’aikatar lafiya ta Jiha kuma ƙwararren likitan iyali, Dakta Joshua E. Moses, yace gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta na yaki da kyama da inganta samun ayyukan kula da lafiyar ƙwakwalwa.
Dakta Moses ya ce ma’aikatar na aiki tukuru don ƙarfafa wayar da kan jama’a game da lafiyar ƙwakwalwa da kuma tabbatar da cewa mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa sun samu kulawa da mutuncin da suka cancanta.
A cewarsa, mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa rukuni ne na musamman da galibi ba a fahimce su kuma ake ƙyama ga su a cikin al’umma, don haka akwai buƙatar ci gaba da wayar da kai.
Yace taken na bana ya jaddada mahimmancin sauraron muryoyin mutanen da suka fuskanci matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa wajen tsara manufofi da shirye-shirye.
Dakta Moses ya yaba wa asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lafia da sauran masu ruwa da tsaki bisa shirya tafiyar, yana mai jaddada cewa hadin gwiwa shi ne ginshikin magance ƙalubalen lafiyar ƙwakwalwa da kuma kawo ƙarshen nuna wariya a jihar.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su nuna tausayi da goyon baya ga mutanen da ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa, yana mai jaddada cewa su ma ɓangare ne na al’umma kuma sun cancanci daidaito a haƙƙi da dama.
