Tinubu ya amince da cigaba da biyan albashin tsofaffin manyan jami’an shige-da-fice har ƙarshen rayuwarsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen yawan samun jinkiri a ƙarin matsayi ga ma’aikatan ma’aikatar da amince wa cigaba da biyan jami’an Hukumar Shige-da-Fice (NIS) masu muƙamin kwantirola janar (CGs) da mataimaka kwantirola janar (DCGs) da suka yi ritaya har zuwa ƙarshen rayuwarsu.

Tunji-Ojo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin rufe taron horo akan Tsarin Ƙwarewar kula da Iyakoki da Shige-da-Fice (BCIMS) da aka gudanar a hedikwatar NIS da ke Abuja.

Ministan ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu bisa warware matsalolin jinkirin ƙarin matsayi, inda ya ce aƙalla jami’ai 50,000 ne suka samu ƙarin matsayi da ofisoshi acikin shekera uku. Haka kuma, ya ce shugaban ya ƙara adadin jami’an da za a riƙa ɗauka zuwa 40,000 a duk lokacin da aka tashi ɗibar sabbin jami’ai. Sannan an ƙara alawus-alawus da ake ba jami’a a matsayin ɓangare na bunƙasa matakin albashinsu.

Ministan cikin gidan ya kuma jinina wa shugaban kan ƙoƙarinsa na faɗaɗa harkokin walwala ga jami’an da ke bakin aiki da waɗanda suka yi ritaya, yana mai bayar da misali da ƙarin kuɗaɗen fansho ga tsofaffin manyan jami’an shige-da-ficen, ta yadda daga matakin karɓar N130,000 a wata, a yanzu an amince da cigaba da biyan su har zuwa ƙarshen rayuwarsu, lamarin da ke nuna ya yi fice cikin sauran shugabannin da aka yi a baya kan walwalarsu.

Kazalika, Tunji-Ojo ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagora mai hangen nesa, wanda an shirya tsare-tsarensa ne domin su yi aiki na tsawon lokaci da tasiri mai amfani akan ma’aikatan gwamnati.

By Babaji

Leave a Reply