(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Mace na iya sayen mai ba tare da sanin cewa abin da yake sa ta ga canjin da take nema shi ne wani sinadari mai ƙarfi da bai kamata ta riƙa shafawa a jikinta haka kawai ba. Wataƙila ba ta san sunan sinadarin ba. Wataƙila ma rubutun kan roban mai ɗin ba shi da cikakken bayani. Abin da kawai ta sani shi ne, wannan cream yana aiki. Kuma a nan ne kalmar aiki take iya zama abu mai cutarwa.
Shin duk wani mai mai saurin kawo canji ga fata ne ya cancanci a kira shi da ingantaccen mai?
Idan fata ta fara rage kauri, ta fara samun tsage-tsage, kuraje ko wasu sauye-sauyen da ba a nema ba a lokacin da ake amfani da mai din da aka kira ingantace, binciken da aka yi kan amfani da kayan sauya launin fata a Afirka ya nuna cewa hydroƙuinone, glucocorticoids da mercury na daga cikin abubuwan da aka samu suna da alaƙa da matsalolin da ake gani bayan amfani da irin waɗannan kayayyaki na dogon lokaci. Daga cikin matsalolin fata da aka ruwaito akwai canjin launi, kuraje, raguwar kaurin fata, tsagewar fata da dermatitis. A wasu yanayi, musamman idan ana amfani da sinadarai masu ƙarfi na dogon lokaci ko a manyan wuraren jiki, akwai kuma yiwuwar matsalolin da suka shafi jiki baki ɗaya.
Bari mu koma ga matsalar haɗa mayuka fiye da ɗaya a shafa a lokaci guda. Ko hakan na tattare da wata illa?
Wannan na daga cikin maganganun da suka fi zama ruwan dare a tsakanin masu amfani da kayan kwalliya. Wata za ta samu cream ɗin da take amfani da shi, ta ƙara wani saboda an ce yana cire tabo, ta ƙara wani saboda an ce yana sa fata ta yi laushi, ko kuma ta haɗa wasu abubuwa saboda ƙawarta ta gaya mata cewa idan an yi haka, sakamakon zai zo da sauri.
Sai dai abinda ya kamata ki sanar da kanki shi ne fata ba wurin gwaji ba ce.
A wani binciken da aka gudanar a Senegal kan illolin amfani da kayan sauya launin fata, kashi 86.5 cikin 100 na waɗanda aka bincika sun kasance suna haɗa abubuwa biyu ko fiye. A cikin wannan binciken, corticosteroids su ne aka fi amfani da su, sannan hydroƙuinone ya biyo baya; an kuma samu matsaloli irin su tsagewar fata da rashin kaurin fata.
Wannan yana nuna mana wani abu mai muhimmanci: wani lokaci matsalar ba wai abin da mace take shafawa kaɗai ba ne. Matsalar na iya kasancewa abin da take haɗawa da abin da take shafawa.
Kuma idan ba ki san sinadaran da ke cikin kowanne daga cikin creams ɗin ba, ta yaya za ki san irin tasirin da haɗin su zai yi?
Wannan shi ne dalilin da ya sa bai kamata a ɗauki shawarar “ki haɗa wannan da wancan” daga bakin mai sayar da kayan kwalliya ko ƙawa a matsayin madadin shawarar ƙwararren likitan fata ba.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, binciken kayayyakin bilicin a wasu ƙasashen Afirka ya nuna cewa abin da ke cikin kwalba ba koyaushe yake dacewa da abin da aka rubuta a jikin kwalbar ba. A wani binciken kayayyakin da aka samu a ƙasashen Yammacin Afirka da Canada, an gano cewa yawan wasu sinadarai kamar mercury, hydroƙuinone da clobetasol propionate a wasu kayayyaki bai yi daidai da abin da aka bayyana a labels ba.
To idan haka ne, ta yaya mace za ta san abin da take shafawa?
Za mu ci gaba.
