Majalisar Dokokin Nasarawa ta amince da samar da ‘yan sandan jiha

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta amince da ƙudirin samar da ‘yan sandan jiha, inda ta zama majalisa ta shida a ƙasar nan da ta amince da gyaran kundin tsarin mulki.

An bayar da amincewar ne a ranar Laraba yayin zaman majalisar a Lafia, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Dakta Danladi Jatau.

Jatau ya karanta sashe 26 na kudin tsarin mulki (Gyara Na Shida) na 2026, wanda majalisar dokoki ta ƙasa ta aikewa majalisun jihohi, kafin ya gabatar da kowane sashe don kaɗa ƙuri’a ta amincewa.

‘Yan majalisar sun amince da dukkan sassan baki ɗaya, inda kakakin majalisar ya bayyana cewa masu goyon baya sun fi rinjaye.

Gyare-gyaren da ake sun shafi wasu sassa na kundin tsarin mulki na 1999, da suka haɗa da sashe na 84, 89, 121, 124, 129, 153, 157, 158, 160, 197, 201, 202 da 204.

Sauran sun haɗa da sauya sashen 214, 215 da 216, da shigar da sabon sashen 317A, gyare-gyare ga sashen 318 da sauye-sauye ga jadawali na biyu da na uku domin samar da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda na tarayya da na jihohi.

Ƙudirin ya kuma ba da shawarar gyare-gyare ga jadawali na biyar da kuma taken kundin tsarin mulkin.

Da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri’ar, Jatau ya yaba wa ‘yan majalisar bisa goyon bayan da suka bayar baki ɗaya tare da umartar akawun majalisar da ya miƙa kudurin majalisar ga Majalisar Dokoki ta ƙasa.

Yace amincewar za ta taimaka wajen cike adadin majalisun jihohin da ake buƙata domin amincewa da ƙudirin kafin ɗaukar wani mataki na gaba.

Majalisar Dokoki ta ƙasa ta miƙa ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki ga Majalisun Dokoki na Jihohi 36 a ranar 16 ga Satumba, 2026, tana neman amincewarsu kan kafa ‘yan sandan jiha tare da ‘yan sandan tarayya.

Idan ba a manta ba majalisar dokokin jihar Nasarawa ta karɓi ƙudirin ne daga akawun Majalisar Dokoki ta ƙasa a ranar 18 ga Satumba, tare da shirin fara duba shi lokacin da ‘yan majalisar suka koma aiki a ranar 28 ga Satumba.

Ƙarƙashin sashe na 9(2) na kundin tsarin mulki na 1999, gyaran kundin tsarin mulki na buƙatar amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin Jihohi, wato jihohi 24 daga cikin 36.

Da wannan amincewar Nasarawa, a yanzu jihohi shida ne suka amince da ƙudirin. Sauran sune Edo, Osun, Oyo, Rivers da Zamfara.

Ana buƙatar ƙarin majalisun jihohi 18 su amince da ƙudirin domin cika sharuɗan kundin tsarin mulki na gyaran da ake nema.

By ukarofi

Leave a Reply