Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce ba zai bayyana matakan da ya ɗauka a ɓoye domin nuna goyon bayansa ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wanda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ke tsare da shi tun watan Fabrairun 2026.
Da yake magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Trust Tɓ, Uba Sani, ya ce har yanzu yana mutunta El-Rufai duk da bambancin ra’ayoyin siyasa.
Ya kuma musanta zargin da ake masa na buƙatar ci gaba da tsare El-Rufai har bayan zaɓen 2027.
Ya ce duk wanda ya yi irin wannan magana, ra’ayinsa yake bayyanawa, ba wai ainahin abin da ya faru ba.
Sani ya bayyana cewa ƙin sukar tsoffin shugabanninsa yana daga cikin halayensa da kuma yadda yake mutunta waɗanda suka riƙe muƙaman gwamnati a baya.
A baya, ’yan siyasar sun kasance abokan juna.
El-Rufai ya goyi bayan zaɓen Sani a matsayin Sanata a shekarar 2019, sannan ya mara masa baya a takarar gwamnan Kaduna a shekarar 2023.
Sai dai dangantakarsu ta yi tsami bayan Uba Sani ya zama Gwamnan Jihar.
Sun samu saɓani kan basuka da gwamnatin Uba Sani ta ce ta gada, binciken da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ta ƙaddamar kan gwamnatin baya, da kuma bambancin ra’ayin siyasa.
A watan Fabrairun 2025, El-Rufai ya bayyana a fili cewa shi da Uba Sani ba abokai ba ne.
Daga baya, ya fice daga jam’iyyar APC, tare da ya komawa jam’iyyar ADC), yayin da Uba Sani ya ci gaba da zama a APC.
An tsare El-Rufai ne bayan da ICPC ta fara bincike a kansa kan zargin aikata laifuka da suka shafi kuɗi.
Hukumar ta zarge shi, tsohon hadiminsa da kamfanoni biyar da hannu a zargin cin hanci da almundahana da kuɗaɗen da suka shafi kwangilar sanya kyamarorin CCTɓ a Kaduna na Naira biliyan 8.68.
Sai dai El-Rufai ya musanta aikata laifin, tare da ƙalubalantar wasu matakai da aka ɗauka a binciken da kuma tsare shi.
