
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026 Fadar Shugaban ta yi kira ga al’ummar yankin arewacin Nijeriya da ta bar yankin kudancin Nijeriya ya kammala wa’adin mulki na shekara takwas domin karrama halin zamantakewa.
Ta ce, ɗorewar al’amuran ƙasa na fuskantar rashin tabbas ne muddin aka gaza samar da haka, inda ta buƙaci shiyyar arewa ta amince da yarjejeniyar baka da aka amince da ita da ta bayar da damar barin ɗan kudu ya kammala wa’adin shekaru takwas tana mai cewa rashin yin hakan ka iya lalata haɗin kan ‘yan ƙasa.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin kafafen yaɗa labarai ta ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajya Rahma Abdulmajid ce ta bayyana haka a Kano yayin taron ƙaddamar da taron Karramawa a Harkar Dabarun Aikin Jarida na ƙungiyar Matan Arewa 4 Tinubu Again (MATA). Ta bayyana cewa, tsarin karɓa-karɓar mulkin Nijeriya ba abu ne na ɓangaranci ba, saidai shi ne ginshiƙin da ya taimaka wa ɗorewar al’amura a jamhuriya ta huɗu wajen cimma nasarorinsu.
Hajiya Rahama ta kuma tunatar da lokacin da aka yi wani gagarumin taro a Kaduna, inda aka cimma yarjejeniyar mulkin karɓa-karɓa wanda a cewarta, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya samu halarta, don haka ba za a sadaukar da ɗorewar al’amuran Nijeriya ba saboda burin mutum guda.
Ta ƙara da cewa, lokacin da mulkin soji ya zo ƙarshe a Nijeriya, an gudanar da wani taron kafa tsarin haɗin kai da ya ƙunshi masu kishin ƙasa, cikin mahalarta har da Atiku Abubakar, kamar yadda sakataren gwamnati (SGF) George Akume ya tabbatar daga bisani. “Cif Sunday Awoniyi, babban dattijon arewa ya miƙe tsaye a 1998 sannan ya ce kada arewa ta bayar da ɗan takara domin maslahar raɗaɗin ‘June 12’ kuma hakan zai warware raɗaɗin kudu,” inji ta.
Kazalika, ta zayyano sauran masu kishin ƙasa da suka goyi bayan wannan fahimta, ciki har da marigayi Dakta Chuba Okadigbo, da ya yi magana a madadin kudu; Alhaji Abubakar Rimi a madadin arewa, Dakta Alex Ekwueme da Dakta Okwesilieze Nwodo. A cewarta, yarjejeniyar ta yi nasara ne bisa karramawar biyayyar da ta samu tun daga lokacin da aka ƙulla yarjejeniyar.

