Gwamnan Zamfara, Musawa, Maryam Abacha, Turai Yar’Adua da wasu sun halarci taron karramawar Tozali

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rukunin Kamfanonin Tozali Media Group ya yi nasarar kammala taron karramawarsa na Henna Ball and Tozali People’s Award na 2026 kuma karo na 8, wanda ya haɗa fuskokin fitattun mutane daga sassa daban-daban na Nijeriya, ciki har da ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, jagororin masana’antu, abokan hulɗa, masu nishaɗantarwa, ‘yan difulomasiyya da ‘yan kasuwa domin yaba wa ƙoƙarinsu, taya su murna da kuma kira ga taimakon al’umma.

Taron wanda aka gudanar a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026 a ɗakin taro na Los Angeles Event Centre da ke Ahmadu Bello Way a Abuja, an shirya shi ne ƙarƙashin taken “Empowering Survivors. Restoring Hope,” wato inganta rayukan waɗanda suka fuskanci matsalolin garkuwa da ta’addanci da dawo musu da karsashin walwala acikin al’umma.

Sannan, taron na shekara-shekarar ya nuna yadda Tozali Media Group take ƙoƙarin amfani da kafar labarai, nishaɗi da damawa da al’umma a matsayin fagagen tasiri acikin zamantakewar al’umma musamman kan kira ga a tallafa wa mata da ‘yan mata waɗanda ayyukan garkuwa, ta’addanci da wasu lamuran rashin tsaro ya shafa kai tsaye.

A wannan karo, taron ya yaba wa wasu mutane da gudummawarsu ga hidimar ƙasa, shugabanci, ayyukan jinƙai, nishaɗi, kasuwanci da ci-gaban ƙasa suka yi gagarumin tasiri acikin al’umma.

Ya samu halartar sanannun mutane, ciki har da Mai Girma Dakta Misis Maryam Sani Abacha, tsohuwar Uwargidan shugaban Nijeriya; Mai Girma Hajia Turai Umar Yar’Adua, tsohuwar Uwargidan shugaban ƙasa; da Sarkin Dutse, tare da wasu sarakunan gargajiya da sauran masu muƙaman sarauta.

Haka kuma, akwai Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal; Uwar taro, Barista Hanatu Musawa kuma Ministar Al’adu da Ƙirƙira da Tattalin Dijital; da kuma shugaban taro, Alhaji Bashir Mohammed Ɗalhatu, Wazirin Dutse. Sannan, akwai Gwamnan Jihar Taraba, Dakta Agbu Kefas, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar da dai sauran wasu fitattun mutane daga sassan ƙasar nan.

Da take jawabi a taron, Shugabar Rukunin Kamfanonin Tozali ta bayyana godiyarta ga muhimman mahalarta, ciki har da jagororin masarautun gargajiya, masu ɗaukar nauyi, waɗanda aka karrama da kyautuka, baƙi da sauransu bisa gudummawarsu wajen samun nasara a taron, tana mai jaddada aniyarsu ta cigaba da jagorantar irin taron domin ƙarfafa wa ayyukan jinƙai da tasirinsu acikin al’umma.

By Babaji

Leave a Reply