Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar neman INEC ta amince da ɓangaren PDP na Turaki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da aka shigar domin tilasta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP, wanda Kabiru Turaki ke jagoranta.

Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa kwamitin alƙalai uku na kotun ne ya yi watsi da ƙarar a ranar Laraba, tare da tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a watan Yulin 2026.

Mai shari’a Ugochukwu Ogakwu ne ya jagoranci kwamitin, yayin da Mai shari’a Laja Balogun da Mai shari’a Ruƙayat Oremei Ayoola suka kasance sauran mambobinsa.

Kwamitin Amintattu (BoT) na ɓangaren PDP da Adolphus Wabara ke jagoranta ne ya shigar da ƙarar.

A watan Yuli, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar neman tilasta wa INEC amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na ƙasa na PDP da Turaki ke jagoranta. Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya yanke hukuncin.

ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1159/2026 ta samu sanya hannun Wabara, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa; Muazu Babangida Aliyu, tsohon Gwamnan Jihar Neja; Jerry Gana, tsohon Ministan Yaɗa Labarai; da Olabode George, tsohon Mataimakin Shugaban PDP na ƙasa.

Sauran waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Maryam Ciroma, tsohuwar Ministar Harkokin Mata; Zainab Maina, tsohuwar Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma; Dame Esther Uduehi, mamba a Kwamitin Amintattun PDP; da ita kanta jam’iyyar PDP.

INEC ce kaɗai aka shigar da ƙara a shari’ar.

Masu ƙarar sun nemi kotu ta bayar da umarnin cewa INEC ta wallafa a shafinta na intanet sunayen mambobin kwamitin riƙon ƙwarya na ƙasa da Turaki ke jagoranta, kamar yadda kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar ya miƙa wa hukumar.

Sun kuma nemi kotu ta tantance ko, bisa tanadin sashe na 32 na kundin tsarin mulkin PDP, INEC tana da wajibcin amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya da NEC ta miƙa mata.

Da yake martani kan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara, ɓangaren PDP na Turaki ya ce ya umarci lauyoyinsa da su garzaya Kotun ƙoli domin neman adalci.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ɓangaren, Ini Ememobong, ya sanya wa hannu, PDP ɗin Turaki ta ce dole ne jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar adawa, ba tare da zama wani ɓangare na jam’iyyar APC mai mulki ba.

Sanarwar ta ce: “Duk da cewa muna mutunta hukuncin kotun, mun ƙuduri aniyar ci gaba da neman adalci bisa gaskiya a Kotun ƙoli. Mun yi imanin cewa ko da an binne gaskiya a wuri mai zurfi, idan masu neman ta suka dage wajen tono ta, wata rana za ta bayyana.”

Ta ƙara da cewa: “Mun umarci lauyoyinmu da su gaggauta shigar da ƙara a Kotun ƙoli, da fatan daga ƙarshe za a yi adalci.”

Hukuncin Kotun ɗaukaka ƙarar na tabbatar da rashin amincewa da ɓangaren PDP na Turaki ya haifar da tambayoyi kan matsayin wasu shawarwarin siyasar da ɓangaren ya ɗauka, ciki har da zaɓen tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takararsa na shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

INEC ta amince da ɓangaren PDP da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta, wanda ke biyayya ga Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).

By ukarofi

Leave a Reply