Yadda ƙarancin lantarki ya tilasta wa mazauna Abuja amfani da sola

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mazauna Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja da dama da masu gudanar da harkokin kasuwanci a sassa daban-daban na birnin sun ce, sun koma amfani da wasu hanyoyin samar da lantarki sakamakon yawan ɗaukewar wuta da kuma rashin samun ingantaccen hasken lantarki tsawon makonni. Wasu daga cikin mazauna yankunan Kubwa, Nyanya, Lugbe, Dei-Dei, Gwagwalada da kewaye sun bayyana hakan yayin da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Abuja, ranar Lahadi.

Da dama daga cikinsu sun ce matsalar rashin wutar lantarki ta shafe sama da makonni uku, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci, lalata kayayyakin abinci masu saurin lalacewa, tare da ƙara wa iyalai nauyin kuɗaɗen gudanar da rayuwa. Saboda haka, mazauna da dama sun koma amfani da hasken rana ta na’urorin Solar da kuma janareto domin samar da wutar da za su gudanar da harkokin kasuwancinsu da ayyukan gida.

Wani ɗan kasuwa mai suna Uche Nwoko, mazaunin Kubwa, ya bayyana yadda ake samar da wutar lantarki a yankin a matsayin abin da ba shi da tabbas ko ɗorewa. Nwoko ya ce rashin daidaiton wutar lantarki ya tilasta masa neman wasu hanyoyin samar da makamashi domin ci gaba da gudanar da kasuwancinsa. Ya ƙara da cewa ƙananan ‘yan kasuwa da ke buƙatar wutar lantarki wajen adana kayayyaki da sarrafa na’urorinsu sun shiga amfani da janareto da na’urorin inverter, duk da yadda farashin man fetur ke ƙara tashi.

Ita ma Rita John, mai sayar da kifin mai ƙanƙara, wadda ke zaune a Kubwa, ta ce rashin wutar lantarkin ya jefa ta cikin matsala wajen adana hajarta, wanda hakan ya tilasta mata kashe ƙarin kuɗi wajen samar da wuta ta wasu hanyoyi, tare da rage yawan ribar da take samu. “Ina sayar da kifi mai ƙanƙara, kuma ina buƙatar samun wutar lantarki a kowane lokaci domin gudanar da kasuwancina. Saboda haka, sai da na kashe kuɗi wajen saka na’urar sola domin adana kayayyakin da nake sayarwa,” inji ta.

A nasa ɓangaren, wani mazaunin Lugbe mai suna Isaac Odigie, ya ce ya koma amfani da sola tsawon shekara guda da ta gabata, bayan shafe shekaru yana fama da ƙarancin wutar lantarki. A cewarsa, amfani da sola ya ba shi damar samun tabbatacciyar wutar lantarki, ba tare da damuwa da halin da wutar lantarkin ƙasa ke ciki ba.

Wani mai aski a Zuba, James Okon, ya bayyana cewa kafin ya koma amfani da sola, yana kashe kusan naira 35,000 duk mako wajen sayen man fetur don janareta. Sai dai ya ce yanzu na’urar sola da ya saka tana samar wa shagonsa da wutar lantarki, ba tare da buƙatar kashe kuɗi mai yawa wajen kula da ita ba.

Haka kuma, wata ƙaramar ‘yar kasuwa mai suna Angela Okafor, mazauniyar Gwagwalada, ta ce ta fara amfani da sola ne saboda yawan katsewar wutar lantarki a yankin da take zaune. Ta bayyana cewa rashin samun wutar lantarki a kai a kai ya shafi kasuwancinta matuƙa, har ta kai ga tana tafiyar da harkokinta cikin asara. “Wutar lantarki ba ta da tabbas. A wasu lokuta, ana samun ta na tsawon sa’o’i biyu ko uku a rana, yayin da a wasu lokutan ba a samun ta kwata-kwata. Tun bayan da na fara amfani da Solar, kasuwancina ya inganta sosai, domin a yanzu ina da abubuwan sha masu sanyi da zan sayar wa kwastomomina a kowane lokaci,” inji ta.

Ita ma Grace Emeje, mazauniyar Dei-Dei wadda ke sayar da abubuwan sha da ruwa, ta ce rashin tabbas wajen samar da wutar lantarki ne ya sa ta koma amfani da sola a kasuwancinta. Emeje ta bayyana cewa da dare, yankin nasu kan kasance cikin duhu, amma tun bayan da ta fara amfani da Solar, shagon ya zama mai haske, lamarin da ke jawo hankalin kwastomomi daga nesa. Ta ce, amfani da Solar ya taimaka wajen bunƙasa kasuwancinta, sabanin a baya da take rufe shagon da wuri saboda rashin wutar lantarki. Ta ƙara da cewa, ‘ya’yanta ma kan je shagon domin yin ayyukan makaranta, kasancewar ba sa samun wutar lantarki a gidansu.

A nata ɓangaren, wani mai ɗinkin kaya a Nyanya, Joseph Ibrahim, ya ce ya koma amfani da sola ne domin samun damar biyan buƙatun kwastomominsa da kuma inganta ayyukan kasuwancinsa. “Na yanke shawarar komawa amfani da sola ne domin cimma burin kasuwancina da kuma biyan buƙatun kwastomomina,” inji shi.

Ibrahim ya ce, tun bayan da ya fara amfani da sola, kasuwancinsa ya samu gagarumin ci gaba, domin yanzu ba ya fargabar katsewar wutar lantarki da ke kawo cikas ga ayyukansa.

By ukarofi

Leave a Reply