Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da rahoton wanzuwar farfesoshin bogi 100 a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026 Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi watsi da rahotannin da ke zargin cewa Hukumar Kula da Jami’o’in Nijeriya (NUC) ta bankaɗo jami’o’i guda 2,000 da kusan farfesoshin bogi 100 a Nijeriya, inda ta bayyana iƙirarin a matsayin “labarin ƙarya mai nufin ruɗar da jama’a da rage darajar tsarin jami’o’in ƙasar”.

Ma’aikatar ta ce, NUC ba ta taɓa bayyana wanzuwar jami’oi 2,000 ba a Nijeriya, wallafawa, amincewa ko tantance wani jaddawalin mutane ba da ake yaɗawa a yanar gizo a matsayin farfesoshin bogi.

Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar ta hannun Daraktar Hulɗa da Jama’ar ma’aikatar, Boriowo Folasade. A ciki ya ce zargin farfesoshin bogi yamutsa hazo ne kan wani rahoto da aka wallafa a ranar 3 ga Disambar 2019, wanda ya shafi aikin NUC na tantance ainihin adadin farfesoshin da ake da su a jami’oin Nijeriya.

A cewarsa, ainihin rahoton bai bayyana sunayen waɗanda ake yaɗawa ba a yanzu, wanda tuni hukumar ta barranta kanta da shi. Ma’aikatar ta koka kan yadda wasu mutane ke yaɗa rahoton bogin, wanda a cewarta ƙoƙarin rage yardar al’umma ne ga harkokin jami’oin Nijeriya da ayyukan ƙarfafa fannin ilimi musamman na tsarin jami’oi.

Akan haka ne ya yi kira ga al’umma, kafafen yaɗa labarai da masu amfani da Soshiyal Mediya da su ƙaurace wa ƙirƙirarren iƙirarin tare da riƙa tantance bayanan da suka shafi jami’oin da aka amince da su da tsarin karatu ta sahihan kafafen yaɗa labaran NUC.

By Babaji

Leave a Reply