Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana nadamarsa kan ƙin amincewa da haɗa tikiti da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce da a ce sun haɗa kai a wancan lokacin, da sun samu damar kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a cibiyar 360 Event Centre.
“Ban fahimci ainihin Peter Obi ba sai yanzu. Da a ce na fi fahimtarsa a shekarar 2023, da mun haɗa kai, mun kuma kori APC daga kujerar shugabancin ƙasa,” inji Kwankwaso, lamarin da ya janyo murna da sowa daga mahalarta taron.
Kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya ƙi amincewa da zama mataimakin Peter Obi, yana mai cewa ya fi shi ƙwarewar siyasa da cancantar ilimi, ciki har da digirin digirgir na PhD.
A lokacin, Kwankwaso ya tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), inda ya zo na huɗu da ƙuri’u 1,496,687, tare da samun nasara a Jihar Kano kaɗai.
Shi kuwa Peter Obi, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP), ya zo na uku, inda ya samu ƙuri’u 6,101,533, tare da samun nasara a jihohi 12, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 25 ga Fabrairun 2023, jam’iyyun adawa sun gabatar da manyan ’yan takara uku, lamarin da ya taimaka wajen samun nasarar ɗan takarar APC, Bola Tinubu.
Tinubu ya lashe zaɓen da ƙuri’u 8,794,726, inda ya kayar da sauran ’yan takara 17.
Jimillar ƙuri’un da Obi da Kwankwaso suka samu ta kai 7,598,220.
Kwankwaso ya gudanar da kamfen a faɗin ƙasar, amma mafi yawan goyon bayansa ya taƙaita ne a yankin Arewa maso Yamma, musamman Jihar Kano, inda ya samu ƙuri’u 997,279, wato kusan kashi biyu bisa uku na jimillar ƙuri’un da ya samu a ƙasa baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, Peter Obi ya samu nasara a yankin Kudu maso Gabas, wasu sassan Kudu maso Kudu, da jihohin Plateau, Nasarawa da Legas, baya ga Abuja.
Kwankwaso ya ce ra’ayinsa ya sauya
A wajen taron na Jigawa, Kwankwaso ya bayyana cewa haɗin gwiwarsu da Peter Obi a zaɓen 2027 wani muhimmin mataki ne na samar da ci gaban ƙasa.
Ya bayyana cewa shugabannin NDC sun cimma matsaya cewa idan suka yi nasara a zaɓen, shi zai jagoranci Ma’aikatar Ilimi domin kawo sauye-sauye a tsarin ilimin ƙasar.
“Zan iya tabbatar muku cewa Peter Obi ya amince zan jagoranci Ma’aikatar Ilimi. Mun cimma wannan matsaya ne bayan na gabatar masa da tsarin bunƙasa ilimi da na aiwatar a lokacin da nake gwamnan Kano, wanda ya yi daidai da irin nasarorin da Mista Obi ya samu a Jihar Anambra,” inji shi.
Kwankwaso ya ce gwamnatin tasu za ta tabbatar da cewa yaran da suka fito daga iyalai marasa ƙarfi sun samu damar karɓar ingantaccen ilimi.
Ya kuma bayyana shirye-shiryen gyara makarantun gwamnati, ɗaukar ƙwararrun malamai da samar da kayayyakin koyarwa na zamani.
Ya ce: “Na riga na nuna hakan a lokacin da nake riƙe da muƙamin gwamnati. Mun ɗauki nauyin karatun ’yan asalin Kano sama da 3,000 a ƙasashen waje, ba tare da karɓar rancen bankunan kasuwanci ko rancen ƙasashen waje ba, kuma ba mu ci bashin ’yan kwangila ba.
“Mun samu damar yin hakan ne ta hanyar yaƙi da cin hanci da rashawa. Wannan shi ne tsarin da muke son aiwatarwa a Nijeriya.”
Haka kuma, ya soki gwamnatocin Kano da Jigawa na yanzu, inda ya zarge su da kauce wa tsarin shugabanci da ya fi mayar da hankali kan muradun al’umma.
Ya kuma jaddada alaƙar tarihi tsakanin jihohin Kano da Jigawa, tare da kira ga al’ummar Jigawa da su goyi bayan tikitin NDC domin samar da mataimakin shugaban ƙasa na farko daga yankin tun bayan samun ’yancin kai a shekarar 1960.
