Daga AISHA ASAS
Akwai bambanci tsakanin mutumin da ya shahara saboda abin da yake yi da kuma wanda ayyukansa suka zama abin da masana ke ganin ya cancanci a zauna a nazarce su, a tantance fasaharsu, a kuma duba gudunmawar da suka bayar ga al’umma. A wasu lokuta, mutum kan shafe shekaru yana gudanar da wani aiki, jama’a suna amfana da shi, amma sai bayan wani lokaci ne ake fara fahimtar irin girman abin da ya bari a baya.
Haka lamarin yake a duniyar adabi, musamman a tsakanin masu waƙoƙin Hausa. Domin waƙa ba ta tsaya ga sauti, kiɗa da nishaɗi kawai ba. A cikinta akwai tunani, harshe, tarihi, al’adu, falsafa da saƙonnin da kan bayyana halin da al’umma take ciki. Wani lokaci ma, waƙa kan zama wata hanya ta isar da saƙon da ba a samu damar bayyana shi ta wata hanya ba.
Wannan ne ya sa labarin wani babban taron ilimi da Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke Jihar Katsina ta shirya domin nazarin rayuwa da ayyukan fitaccen mawaƙi kuma marubucin Hausa, Alhaji Aminu Ladan Abubakar, Sarkin Adabin ƙasar Hausa, wanda aka fi sani da Alan Waƙa, ya cancanci kulawa ta musamman.
Taron, wanda aka sanya wa suna 1st International Conference on Aminu Ladan Abubakar (ALA) 2026, an tsara shi ne domin tattauna fasahar waƙoƙinsa da sauran rubuce-rubucensa, tare da nazarin ginshiƙai da ƙa’idojin adabin da ya gina ayyukansa a kansu.
Bisa sanarwar shirya taron, an tsara gudanar da shi daga ranar 8 zuwa 11 ga Nuwamba, 2026, a harabar jami’ar da ke Dutsin-Ma, Jihar Katsina, tare da tsarin halartar taron kai tsaye da kuma ta yanar gizo.
Taken taron shi ne, “The Poetics of Aminu Ladan Abubakar’s Literary Works: A Study of Theory and Principles of Literary Composition.” Wato nazarin fasahar adabi a cikin ayyukan Aminu Ladan Abubakar, tare da duba ka’idoji da ginshiƙan da suka tsara rubuce-rubucensa.
Wannan sanarwa ta bayyana cewa taron shi ne irinsa na farko da aka ware musamman domin nazarin ayyukan adabin ALA a matakin taron ilimi na ƙasa da ƙasa. An shirya shi ne ta haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Harshen Hausa, Tarihi, da Adana Takardun Dijital na Sashen Hausa na jami’ar.
A ranar 1 ga Agusta, 2026, jaridar Peoples Daily ta wallafa rahoton amincewar shugaban FUDMA na shirya wannan babban taro.
Rahoton, wanda Sabitu Muhammad ya rubuta, ya bayyana cewa an samu amincewar ne bayan ziyarar girmamawa da Alan Waƙa da wasu mambobin kwamitin shirya taron suka kai wa mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Mohammed Khalid Othman.
A yayin wannan ganawa, Farfesa Othman ya bayyana muhimmancin taron wajen zurfafa bincike kan adabin Hausa, waƙoƙi da rubuce-rubucen fasaha. Ya kuma bayyana cewa taron zai zama wata dama ta nuna arzikin harshen Hausa da gudunmawar masana da sashen Hausa na jami’ar ke bayarwa.
Shi ma shugaban tsangayar Fasaha, Farfesa Bashir Aliyu Sallau, ya bayyana taron a matsayin wani babban taron tarihi, tare da yabawa shugaban jami’ar bisa goyon bayan da yake bayarwa wajen bunƙasa binciken ilimi da al’adun gargajiya.
A cikin wannan ganawa, mataimakin shugaban jami’ar mai kula da harkokin ilimi, Farfesa Abubakar Sadiƙ Suleiman, ya bukaci mambobin kwamitin shirya taron su yi aiki tare cikin haɗin kai.
Haka kuma, magatakardan jami’ar, Dakta Musa Ajiya, ya yi kira da a guji cakuda Hausa da Turanci ba tare da dalili ba yayin gabatar da takardun bincike da jawabai na hukumance.
A nasa jawabin, Alan Waƙa ya nuna godiya ga jami’ar bisa wannan karramawa, tare da bayyana fatansa cewa taron zai ƙarfafa matasa marubuta, mawaƙa da masu bincike wajen kiyaye da bunƙasa al’adun adabin Hausa.
Wannan rahoto ya nuna cewa shirin taron ya samu goyon bayan shugabannin jami’ar tun kafin lokacin gudanar da shi.
Duk da cewa mutane da dama sun fi sanin Aminu Ladan Abubakar a matsayin Alan Waƙa, bincike ya nuna cewa gudunmawarsa a adabin Hausa ba ta fara daga waƙoƙin da yake rerawa ba.
A wata maƙala da Abdullahi Mujaheed ya rubuta a shekarar 2021, mai taken Aminu Alan Waƙa a Fagen Rubutattun ƙagaggun Labarai na Hausa, wadda aka wallafa a mujallar Algaita: Journal of Current Research in Hausa Studies, an yi nazari kan gudunmawar da ALA ya bayar a fagen rubutattun labaran Hausa.
Maƙalar ta bayyana cewa Alan Waƙa ya fara ne a fagen rubutun ƙagaggun labarai kafin ya fi samun shahara a waƙoƙin zamani.
Wannan muhimmin bayani ne domin yana nuna cewa ba za a fahimci cikakken fagen fasaharsa ta hanyar duba waƙoƙinsa kaɗai ba. Akwai kuma rubuce-rubucen ƙagaggun labarai da suka ƙunshi saƙonnin gyaran halaye, faɗakarwa da ƙarfafa riƙo da kyawawan ɗabi’u.
A cikin wannan bincike, an ambaci wasu daga cikin littattafan da ya rubuta, ciki har da ‘Jirgi ɗaya’, ‘Baƙar Aniya’, ‘Cin Zarafi’, ‘ƙawa Zuci’ da ‘Tarzoma’.
Abin lura a nan shi ne yadda binciken ya nuna alaƙar saƙonnin da ke cikin littattafansa da waɗanda yake isarwa ta waƙoƙinsa. Wato, tun kafin ya zama sananne a matsayin mawaƙi, akwai alamun cewa yana amfani da rubutu wajen bayyana ra’ayoyi da faɗakar da al’umma.
Wannan yana ƙara bayyana dalilin da ya sa nazarin ayyukansa ya kamata ya shafi rubuce-rubuce da waƙoƙi baki ɗaya.
Wani bincike da ya ƙara fito da matsayinsa a duniyar adabin Hausa shi ne takardar da Shuaibu Hassan ya rubuta mai taken A Critical Analysis of Baubawan Burmi, Kassasaɓarmu Ce Kan Zaɓar Jagora by Aminu Ladan Abubakar (ALA).
An wallafa binciken a mujallar Studies in African Languages and Cultures, mujalla ta 55, a shekarar 2021.
Binciken ya mayar da hankali kan waƙar ALA mai suna Baubawan Burmi, Kassasaɓarmu Ce Kan Zaɓar Jagora, inda aka nazarci yadda mawaƙin ya yi amfani da waƙa wajen nishaɗantarwa da kuma isar da saƙon siyasa ga masu sauraro.
A cewar binciken, waƙar ta ƙunshi saƙonnin wayar da kan masu zaɓe game da shugabanci da kura-kuran da ake iya aikatawa wajen zaɓen waɗanda za su jagoranci al’umma.
Wannan ya nuna cewa waƙar Hausa za ta iya zama hanyar ilimantarwa da tattauna matsalolin al’umma, ba wai hanyar nishaɗi kawai ba.
Wani misali kuma shi ne binciken Dabo’s Bow: An English Rendition of Bakan Dabo by Aminu Ladan Abubakar (ALA), wanda aka wallafa a Ondo Journal of Arts a shekarar 2025.
Binciken ya yi nazari kan waƙar Bakan Dabo, wadda ta shafi yabon marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. Masu binciken sun yi nazarin ma’anar kalmomin waƙar, alaƙarsu da tarihin sarautar Kano da kuma yadda ake amfani da wasu kalmomi wajen ɗaukar ma’anoni masu zurfi a adabin Hausa.
Abin da wannan bincike ya ƙara nunawa shi ne cewa waƙoƙin ALA suna ɗauke da abubuwan da za a iya nazarta ta fuskokin harshe, tarihi, al’adu da kuma fasahar gina waƙa.
A ranar 28 ga Agusta, 2026, an wallafa wani bincike mai taken Tauraron Mawaƙa: Aminu Ladan Abubakar a Faifan ɗaukaka.
Mawallafan binciken su ne Dakta Abu-Ubaida Sani na Jami’ar Tarayya ta Gusau da Musa Suleiman na Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies, Kano.
An wallafa binciken a mujallar Njinga & Sepé: Revista Internacional de Culturas, Línguas Africanas e Brasileiras, mujalla ta shida, ƙarin na musamman na biyu, shafuka na 292 zuwa 312.
Masu binciken sun yi amfani da ra’in tasirin taurari a kan al’ada (Celebrity Theory of Culture) wajen nazarin yadda ALA ya yi fice da kuma tasirin da shahararsa ta yi a duniyar waƙoƙin Hausa.
Binciken ya bayyana cewa baiwarsa, ƙwarewarsa da kuma yadda yake mu’amala da masu sarauta, attajirai da malamai sun taimaka wajen bunƙasa shahararsa.
Abin da ya fi muhimmanci a cikin wannan takarda shi ne shawarar da masu binciken suka bayar ta shirya babban taron ƙara wa juna sani domin nazarin rayuwa da ayyukan ALA baki ɗaya.
Wannan shawara ta yi daidai da manufar babban taron da FUDMA ta shirya a wannan watan nan na Nuwamba.
Wato, kafin a sanar da taron FUDMA, akwai binciken ilimi da ya riga ya nuna buƙatar samun irin wannan taro na masana.
Wani ɓangare na rayuwar ALA da ya ƙara jan hankalin jama’a shi ne sarautar da aka naɗa masa ta Sarkin Adabin Harshen Hausa.
A wani rubutu da Kabiru Yusuf Fagge ya wallafa a New Citizen Hausa ranar 13 ga Fabrairu, 2026, an bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Daura ya naɗa Alhaji Dakta Aminu Ladan Abubakar a matsayin Sarkin Adabin Harshen Hausa.
Rubutun ya kuma bayyana cewa an naɗa Alhaji Dauda Adamu Kahutu, wato Rarara, a matsayin Sarkin Mawaƙan ƙasar Hausa.
Duk da cewa wannan batu ya jawo muhawara a tsakanin wasu masu bibiyar al’amuran adabi da sarautun gargajiya, musamman game da ma’anar waɗannan sarautu da iyakokin ikonsu.
Abin da za a iya tabbatarwa daga rahoton shi ne cewa an bayyana ALA da wannan sarauta, kuma hakan ya ƙara fito da matsayinsa a fagen adabin Hausa.
Duk da haka, darajar aikinsa ba za ta tsaya ga sunan sarautar da aka ba shi ba. Muhimmin abin dubawa shi ne irin gudunmawar da ya bayar a rubuce-rubuce, waƙoƙi da kuma yadda ayyukansa suka zama abin nazari ga masana.
Me ya sa wannam taron ke da muhimmanci ga adabin Hausa?
Za mu ci gaba mako mai zuwa.
