Zallawa na son dawo da ashar Arewa?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Allah ya raba mu da sharrin Zallawa don wallahi wasu ƙazaman ashar da a ka daina jin su, yanzu ‘yan ƙulla mairci na soshiyal midiya sun dawo da su! Bayyanar waɗannan gwarawa masu iƙirarin Hausa zalla ya dawo da manya-manyan ashar masu maiko da a ka daina jin su gabanin tarbiyyar addinin Musulunci ta karaɗe birane da ƙauyuka. Kai addinin Kirista ma bai amince da ashar ba. Duk wanda ya taso a Arewa ko ba musulmi ba ne za ka ga ya koyi wakilin-zagi irin DAN NEMA, DAN BUTAN UWA, TASONO da sauransu inda ashar mai maiko na batsa ko a mafarki an daina tunowa da su. Wallahi bayyanar Zallawa a soshiyal midiya ta dawo da ashar na mutane masu ƙazamar zuciya, rashin tarbiyya da mutunci. Akwai takaici ainun da wacannan miyagun mutane ke makalewa da sunan Hausawa duk da akasrinsu na yayata mugun nufin ne a shafukan yanar gizo na bogi don su ɓoye asalinsu da dabarar kar a gano su waye ne.

Za ka ga dan bazata maƙiyin Hausawa da ya yi shigar burtu wai Bahaushe ne ya zunduma ashar da kuma kushe addini don dama shi addini ya wargaza kafircin danginsu! Wai zagin ma marar kan gado shi ne UBAN BABANKA sai kuma na ‘yan sholisho HEGU, Shaggu da sauran salon kalamai daga tsamin bakin gwarawa da su ka tsintsi Hausa a yawon dandi. Yaya ma mutumin kirki duk yadda ya tunzura zai ambata “Ku ci uwarsu”..don mai kaza da kaza! Haƙiƙa waɗannan mutanen duk ba Musulmi ba ne ko kuma fasikai ne.

Idan ba mai karin kumallo da farfesun bera ko kafar kare 404 ya kora uwar laifi KHAMRU ba, ai wata maganar cikata ta sai Bulus “Don cika dan ƙoƙon giya wannan iya aikin sai Bulus..” ko su Thomas Angulu mai Rotimas da Benson.

Indai ka ga zagi ba sakayawa to masu ikirarin Hausa zalla ne da a ka ɗauka kwangila don wargaza Arewa da zummar cimmawa AIFOB da Midil bel muradun aware. A wajensu kaɗai za ka ga an dubi mai alfarma sarkin musulmi an zunduma ma sa ashar, su dubi malamin Alkur’ani da Hadisi su ci ma sa mutunci yayin da su ke murɗe wuyan tarihi. Mu na da shaidun hatta yadda su ke amfani da wani zane wai Shehu Mujaddadi ne su daura shi kan dalar gawawwaki don kawai su nuna Musulunci addini ne na zubar da jini. Akwai hotunan da su ka yi amfani da hoton mai alfarma sarkin musulmi su ka cusa ma sa katuwar kwalbar giya a baki. Kai annanci mugun yanayi ne da in mutun ya tsinci kansa cikin mumunai ya yi ta hamdala, alwala da raka’a ko biyu ne na nafila.

Duk wata hanya ta kure tayar iskanci, wadannan mutanen sun kai ganiya inda kuma don rainin hankali sai su rubuta wai don sun ce za su kafa ƙungiya ne shi ya sa a ke yi mu su cancagoli. Haba wa ke maganar ƙungiya idan a na maganar marar sa tarbiyya ‘yan kwangila masu zunduma ashar ba kunyar dattawa balle Allah mahaliccin sammai da ƙassai. Ko Baibul din za su yi amfani da shi yadda ya dace bai koya mu su zagi ba.

Haba haka kawai wasu wawaye za su karɓo kwangila daga AIFOB kuma su shiga rigar Hausawa don rusa arewa! Arewa ta hausawa ce da al’ummar Hausa kuma duk mai adawa da Arewa babban maƙiyin Hausawa ne

Kamar yadda Allah maɗƙukakin Sarki ya saukar da Alƙur’ani cikin harshen Larabci kuma hakan ya ƙarawa harshen albarka da zama mafi daraja ga dukkan Musulmi, hakanan Allah ya ɗaukaka harshen Hausa a tsakanin harsunan Afurka don yadda a ke wa’azin Islama da harshen. Wallahi wannan shi ya sa duk makiya Musulunci su ka tsani harshen da ɗƙukar duk mai amfani da harshen a matsayin abokin hamayyarsu. ABOKI, Malam, Malo, Mumu, Almajiri, Jihadists da sauran kalmomi na zayyana Hausawa a karkace na fitowa ne daga bakunan waɗanda yau ke cewa sun haɗa kai da masu karyar Hausa zalla don ƙwato wai haƙƙin Hausawa da a ka danne! Wa ya danne kuma me a ka danne? Maƙaryata ne kawai da ke ƙin jinin Musulunci.

Yau an wayi gari za ka ɗan AIFOB ya hau soshiyal midiya ya na rashin kunya ga Sarkin Musulmi da jefa ma sa kalmomi na sharri da wulaƙanci inda ‘yan barandar AIFOB din masu karyar wai Hausawa ne alhali aljifan baya ne sai su shigo su na zunduma ashar ga Shehu Mujaddadi da sauran manyan malaman Musulunci amma sam ko sau ɗaya ba za ka taba ganin sun zagi wanda ba musulmi ba. Wannan aikin sai Kadamusawa. In ka ja kunnensu sai wani dan sullutun yaro da ko majina bai goge a hancinsa ba ya yi saraf ya ce wai an daina yaudarar Hausawa yanzu karni na 21 ne. Haba a ɗauri kashi ko a ɓata igiya.

Wallahi na sha bayyanawa a nan kafar cewa ina wannan rubutun ne ba don ‘yan kwangilar rusa Arewa ba, a a ina yin hakan ne don ankarar da matasa da ka iya ruɗuwa da ƙaryar masu iƙirarin Hausa zalla kar su fada tarkonsu na makircin neman kuɗi da yaki da Musulunci. Ba yadda za a yi Bahaushe usul na gaskiya ya shiga wannan sabgar da rusa kai da kai. Haba ai abun kunya ne ma a ce wai AIFOB ce za ta ceci wani a Arewa. Idan kura na da maganin zawo ta yi kanta ma na yau ina madugun AIFOB ɗin ina kuma dan karambani na ƙasar New Zealand.

Mutanen da ba su iya Hausa ba kuma ba su damu da dokokin Musulunci na hani da makirci, don dama makiya addinin ne, kuma su fito a soshiyal midiya ba hoto ba sunan gaskiya, maza su koma mata kuma wai wani har ya yarda da abun da su ke fada. Ha ha wallahi ƙaryarsu ta sha karya kuma in Allah ya yarda za a kai ga lokacin da hukuma za ta shiga cafke duk mai alaka da AIFOB. Kowa ya san kotu da gwamnatin Nijeriya sun ayyana AIFOB a matsayin haramtacciyar ƙungiya mai ayyukan ta’addanci. Ko jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu an yanke ma sa hukuncin ɗaurin rai da rai bayan kotu ta same shi da laifin ta’addanci da cin amanar ƙasa. Don haka a zahiri duk mai goyon baya ko bin salon AIFOB na karantsaye ne ga dokokin ƙasa kuma tabbas doka ka iya nuna hushinta a kansa.

Tsarin mulkin ƙasa ya ba wa kowa dama ya zauna inda ya ga ya dace ya kuma yi addinin da ya yi imani da shi amma a lokaci guda tsarin bai ba wa kowan mahaluki damar fakewa da addininsa ko ‘yancinsa wajen cin zarafin wani ko ɓata ma sa suna don cimma wata manufa ta bayan fage ba. Mun ga ai yadda doka ta ajiye matsayin ‘yan ƙungiyar AIFOB a haramtattu.

Gaskiyar magana a ‘yan kwanakin nan na ga Zallawa sun haƙiƙance sai sun shigar da shubuha kan asalin fitinar jihar Filato wacce ta addini ce da ƙabilanci kuma ba ma lallai sai an kawo batun faɗan makiyaya da manoma ba. Haƙiƙa akwai hannun Beromawa dumu-dumu a shigar burtu da rigar Hausawa don yin rufa-rufa kan rayukan da su ka sheke a tsawon shekaru ba tare da yin nadama ko ma neman ahuwan iyalan mutanen da ba gaira ba dalili su ka salwantar da rayukan su.

Misali kawai na ke yi da Janar Alƙali wanda haka kurum ‘yan ina da jini su ka tare a Dura-Du Jos ta kudu su ka kashe shi da wurga motarsa cikin kududdufi. Hatta lokacin ƙoƙarin nemo gawarsa da su ka turbude a wani rami na wulaƙanci sai da iyayensu mata su ka yi caa wai za su yi tsirara matuƙar an matsa lamba sai an nemo gawar. Shin a mota a ka tare Janar Alƙali ko shanu ya ke kiwo ya auka gonar Ba-Birome a Dura-Du don haka ya cancanci kisa?

Daliban Shehu Dahiru Bauchi da su ka zo wucewa a tawagar motocinsu rike da tasbaha, haka mugayen mutanen nan don ƙiyayyar bambancin addini su ka tare su, su ka kashe su har da daukar kisan a faifan bidiyo don nunawa duniya ba yadda za a yi su bari Musulmi su zauna kai ko ma su rika wucewa salun-alun ta yankin Filato.

Kuma haka mu ka ji labari kwatsam na wasu Zazzagawa da su ke je ɗaukar aure Filato amma maimakon a taimaka mu su da nuna hanya sai mugayen mutanen nan su ka sheƙe su! Shin su ma kiwon shanu su ke yi ko farmaki su ka kai wa wani kauyen Beromawa har su ka cancanci a kashe su? Wallahi waɗannan misalai ne a cikin labarun kisan gilla da yawa da mutanen nan maƙiya zaman lafiya su ka aikata kuma ba nadama sai ma ƙoƙarin nunawa duniya wai su a ke cutarwa!

KAMMALAWA

A soshiyal midiya na ga Beromawa da masu ba su kariya na cewa wai a bar Beromawa su murkushe makiyaya wai don Fulani sun zama annoba! Janar Alkali da sauran jama’a shanu nawa su ka shigar Filato? Ba wanda za a rainawa hankali sai mai ƙarancin nazari.

Daɗin abun al’ummar Jasawa sun yi watsi da mugun nufin Zallawa don sun san dalilan rikicin jiharsu saboda mai ɗaki shi ya san inda ke yi ma sa yoyo.

Karatun ya fito tas?

By ukarofi

Leave a Reply