Daga UNCLE LARABI
Auren Bahaushe na wannan zamanin uwar matar ita ke bayar da gudunmawa wajen ruguza shi. Kaɗan daga cikin ɗumbin matsalolin Bahaushe a cikin aure shine; kallafa wa namiji komai shi zai yi ita kuma mace ta kwanta ta ci bulus. ‘Yar biyayyar da a da ake cewa mace ta yi wa namiji yanzu ta juye namijin ake so ya haɗa ya dinga yi wa mace.
Da za mu dawo cikin hayyacinmu da mun gane cewar, aure ba wai nauyi ne na komai ga mutum ɗaya ba, kowa yana da rawar da zai iya takawa, don ganin ya bayar da irin tasa gudunmawar komai ƙanƙantarta. An wanke wa mata ƙwaƙwalwa da cewar; namiji ne zai yi musu kyauta, su ba za su yi ba ko suna da Fam taɓa-sama. Naka kuɗin shine na ci, nasu kuma na adanawa.
Wani shirmen da mata suka sake jefa kansu a ciki wanda yake taka muhimmiyar rawa wajen ruguza aure shine; wai namiji ne zai basu kulawa. Shi zai dawo daga ofis ko kasuwa ko wajen aikin ƙarfi cike da gajiya da tunani barkatai a ƙwaƙwalwarsa, wanda yana son ya samu nutsuwa da kulawa da kwanciyar hankali, ita kuma Lami a lokacin take zumɓure-zumɓuren baki da ɗaure fuskar wai ya dawo gida bai ba ta kulawa ba.
Tabbas akwai babban aiki a gare mu cikin zamantakewar aure a ƙannan zamanin. A irin wannan yanayin ne yarinya Lami za ta ɗauki waya ta kira uwarta tana kuka, wai Sadam ya dawo daga kasuwa ko aiki ko ƙwadago kuma ya yi shiru bai ba ta kulawa ba. Nan za ka ji Ramatu uwar Lami ta kwashi salati tana cewar; ai ba ki yi sa’ar miji ba, ki yi haƙuri, maimakon ta faɗa mata cewar; ai ke ce ya fi cancanta ki je ki sauke girman kai ki ba shi kulawa, ki sanya ya manta dukkan damuwar da ya shigo da ita cikin gidan.
A wannan zamanin da muke ciki duk auren da ka ga ya mutu, to a kaso 100, kaso 65 akwai sa hannu da gudummawar uwar yarinyar da aka saka ɗin.
Uncle Larabi (wato Abdullahi Jibril Dankantoma), mariubuci ne a jihar Kano, Nijeriya. Za a iya samun sa a 08065418892,
23 ga Satumba, 2026
