Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wata ƙungiya mai zaman kanta, Zamfara Integrity Group, ta ƙalubalanci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya rantse da Allah kan asalin kuɗin da yake amfani da su wajen kamfen ɗin neman sake zama Gwamna cewar ba kuɗin gwamnatin jihar bane.
A cikin sanarwar da ta rabawa manema labarai, wadda shugaban ƙungiyar na Jihar, Muhammad Sagir, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya fito fili ya bayyana cewa kuɗin kamfen ɗinsa ba daga baitul-malin jihar ba ne.
“Kuɗin kamfen ɗin da kake rabawa, kuɗin jama’a ne ko kuɗin ka ne na ƙashin kai muna son kowa ya sani?”
Ƙungiyar ta ce matsayinta abu ne mai sauƙi kuma na kundin tsarin mulki, tana cewa kuɗin jama’a don ayyukan jama’a ne, kuɗin mutum kuma don ayyukan mutum ne na kashin kai.
A cewar sanarwar, babu wani mai riƙe da muƙamin gwamnati, musamman Gwamna, da aka yarda ya yi amfani da kuɗin jama’a wajen gudanar da kamfen.
Ta bayyana cewar Gwamna na iya kashe kuɗin sa na kashin kai a ayyukansa na siyasa, amma bai kamata ya kashe ko sisi ɗaya daga baitul-malin jama’a ba.
“Kuɗin jama’a na dukkan alummar Jihar Zamfara ne ba na ‘yan APC ba, ba na wata jam’iyyar siyasa ba, kuma ba na kamfen ɗin wani Gwamna ba,” in ji kungiyar.
Ƙungiyar ta kawo sashe na 162 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara), wanda ya kafa asusun tarayya kuma ya tanadi yadda za a raba kuɗaɗen jama’a ga Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi don ayyukan jama’a.
Ta yi jayayya cewa kundin tsarin mulki bai tanadi wata dama wajen kashe su a yaƙin neman zaɓen gwamna ba.
Ta kuma kawo sashe na 15(5) na kundin tsarin mulki, wanda ya wajabta wa Jiha ta kawar da cin hanci da rashawa, tana gargaɗin cewa Gwamnan da ya karkatar da kuɗin jama’a wajen gudanar da kamfen ya saɓa wa kundin tsarin mulki, ya ci amanar jama’a, kuma ya karya rantsuwar ofishinsa.
“Kuɗin jama’a ana riƙe da shi ne a matsayin amana ga jama’a; mayar da shi kuɗin kamfen cin amanar jama’a ne kuma karya rantsuwar ofishi ne.” Ƙungiyar ta ƙara da cewa.
Ƙungiyar ta tunatar da cewa Gwamna Lawal ya sha faɗin cewa ba zai iya amfani da kuɗin jama’a ba, kuma gwamnatinsa ba za ta ba mutane kuɗi ba.
“Ya Zama wajibi Gwamna Dauda Lawal ya wanke kansa kuma ya kawar da shakku a zukatan alummar Jihar Zamfara cewar ba kuɗin baitulmalin jihar yake kashe wa ba a lokacin yaƙin Neman zaɓen sa.”
Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnan da ya rantse da Allah a wajen kamfen ɗinsa cewa duk kuɗin da zai kashe a kamfen ɗinsa, daga farko har zuwa ƙarshe, kuɗin sa ne na kashin kai ba kuɗin jama’a ba.
Baya ga kuɗin kamfen, ƙungiyar ta kuma tunatar da Gwamna Lawal alƙawarin da ya yi a lokacin kamfen ɗin 2023 na kawo ƙarshen matsalar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Zamfara.
Ta yi kira ga manema labarai, ƙungiyoyin farar hula, shugabannin addini da al’ummar Jihar Zamfara da su saurari bayanin Gwamna a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen sa tare da yin hisabi bisa kundin tsarin mulki da alƙawuran da ya ɗauka.
