An fitar da marubuta uku da suka kai matakin ƙarshe a gasar littattafan matasa ta TY Buratai ta 2026

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Gasar kyautar rubuce-rubucen littattafan matasa ta TY Buratai Literary Initiative (TYBLI) ta fitar da sunayen marubuta uku da suka kai matakin ƙarshe a gasar ta shekarar 2026.

Marubutan sun fito ne daga cikin sama da ayyuka 100 da aka miƙa domin tantancewa, inda aka bi matakai daban-daban kafin zaɓen waɗanda suka kai matakin ƙarshe.

Waɗanda suka samu wannan dama sun haɗa da Yemi Hanson, marubuciyar ‘Let Us Tell This Story’, wadda ta wakilci yankin Kudu maso Yamma.

Sauran su ne Umar Ibrahim, marubucin ‘A Hundred Lashes’, daga yankin Arewa ta Tsakiya, da kuma Chinenye Chizitere Opara, marubuciyar ‘A Lady in Bloom’, wadda ta fito daga yankin Kudu maso Gabas.

Waɗannan marubuta uku sun samu nasarar shiga matakin ƙarshe ne bayan tantance ayyukan marubuta shida da suka yi nasara a matakin shiyyoyi daban-daban na Najeriya.

Kowanne daga cikin marubutan shida da suka yi nasara a matakin shiyyoyi ya samu kyautar kuɗi Naira 500,000, kafin a zaɓi mutum ɗaya daga cikin ukun da za a bai wa babbar kyautar gasar.

An tsara sanar da wanda ya lashe gasar a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, yayin bikin bayar da kyaututtukan da shirin ya shirya.

Gasar na daga cikin shirye-shiryen ƙarfafa rubuce-rubucen littattafan matasa a Najeriya, musamman ta hanyar samar da dama ga marubuta daga sassa daban-daban na ƙasar domin su nuna fasaharsu.

By ukarofi