Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da motocin ƙungiyar matasan Katsina na yaƙin neman zaɓen 2027

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da shirin bayar da motocin tallafi na ƙungiyar Katsina North Youth Development and Awareness Initiative (KNYDAI), domin taimaka wa harkokin sufuri da tsara ayyukan yaƙin neman zaɓe a matakin ƙananan hukumomi a shiyyar Sanatan Daura, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kamar yadda kafar sadarwa ta JBC ta ruwaito, Gwamna Radda ya gode wa shugabannin ƙungiyar, mambobinta da magoya bayanta bisa jajircewa da gudummawar da suke bayarwa wajen ƙarfafa ayyukan yaƙin neman zaɓe.

Ya ce motocin za su taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga, daidaita ayyuka da ƙarfafa hulɗa da al’umma a ƙananan hukumomin shiyyar.

Gwamnan ya kuma yaba wa babban uban ƙungiyar, masu gudanar da ayyukanta da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bayarwa, inda ya buƙace su da su ci gaba da haɗin kai da jajircewa.

Tun da farko, babban uban ƙungiyar, Sarkin Fadan Daura, Alhaji Lawal Sade, ya jaddada muhimmancin haɗin kai da shigar matasa cikin harkokin tallafa wa manufofin yaƙin neman zaɓe.

Ya bayyana cewa bayar da motocin wata gudummawa ce ta zahiri da za ta taimaka wajen inganta hulɗa da al’umma da kuma daidaita ayyukan yaƙin neman zaɓe a faɗin shiyyar.

A wani ɓangare na ayyukan raya ƙasa, Gwamna Radda ya kuma aza harsashin gina katafaren kasuwa ta zamani a garin Daura.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mataimakin Gwamnan Jihar, Malam Faruk Lawal Jobe; tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika; tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, Dakta Mustapha Inuwa; Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Dikko/Jobe, Arc. Ahmed Musa Dangiwa; Mataimakin Darakta Janar, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir; Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Hon. Nasiru Yahaya Daura; Shugaban APC na jihar, Dakta Bashir Gambo Saulawa; da sauran jami’an gwamnati.

By ukarofi