Sanatar Legas ta rasu bayan sa’o’i da bikin cikarta shekeru 56

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanatar da ke wakiltar Mazaɓar Legas ta Yamma, Dakta Idiat Adebule ta rasu ƙasa da kwana guda da kammala bikin zagayowar ranar haihuwarta ta cikarta shekera 56 a duniya. Adebule, wadda tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan jihar Legas ce, an sanar da mutuwarta ne a wani asibitin kuɗi da ke yankin unguwar GRA a Ikeja, Jihar Legas.

Wata majiya mai kusanci da marigayiyar ce ta tabbatar da rasuwarta ga ‘yan jarida a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, saidai ba kai ga sanin ainihin abin da ya sabbaba mutuwar ba yayin haɗa wannan rahoto.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mambobin gundumarta suke shirin aiwatar da gangamin yaƙin neman zaɓe a ranar Litinin, 30 ga Nuwamba, a matsayin ɓangare na harkokin zaɓukan 2027 da ke tafe.

A ranar Juma’a Adebule, wadda ke neman sake zaɓe a karo na biyu a Majalisar Dattawa, ta rasu tana da shekara 56 a duniya bayan wallafa saƙon godiya ga Ubangiji a Soshiyal Mediya kan damar da ya ba ta na hidimta wa al’umma.

By Babaji

Leave a Reply