Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa (NHRC) ta bayyana cewa ta samu koke-koken take haƙƙin ɗan Adam sama da miliyan 2.5 a faɗin Nijeriya tsakanin watan Janairu da Oktoba na shekarar 2026.
Hukumar ta kuma bayyana cewa a cikin watan Oktoba kaɗai ta samu koke-koken cin zarafin cikin gida 1,873, auren dole 376 da kuma fataucin mata 339.
Babban sakataren hukumar, Dakta Tony Ojukwu, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da ayyukan hukumar na ƙasa baki ɗaya domin bikin wayar da kan jama’a na kwanaki 16 kan yaƙi da cin zarafin mata da ’yan mata na shekarar 2026.
Gangamin na bana na gudana ne ƙarƙashin taken: “Mu haɗa kai wajen kawo ƙarshen cin zarafin mata da ’yan mata: A tabbatar da adalci, a kare waɗanda aka zalunta, a kawo ƙarshen rashin hukunta masu laifi.”
Ojukwu ya ce, cin zarafin mata da ’yan mata ba matsalar zamantakewa ce kawai ba, illa take haƙƙin zan Adam ne da ke tauye mutuncinsu, daidaito da ’yancinsu na rayuwa ba tare da tsoro, wariya ko cin zarafi ba.
Ya jaddada cewa yaƙi da matsalar na buƙatar fiye da furta kalaman Allah-wadai, domin dole ne a samar da hanyoyin samun adalci cikin sauƙi, kariya ga waɗanda aka zalunta, hukumomi masu sauke nauyinsu da kuma hukunta masu laifi.
A cewar shugaban hukumar, alƙaluman da ke cikin kundin bayanan hukumar na wata-wata kan yanayin haƙƙin ɗan Adam sun nuna cewa an samu koke-koken take haƙƙi sama da miliyan 2.5 daga ofisoshin hukumar da ke jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja, tsakanin Janairu da Oktoba 2026.
Alƙaluman watan Oktoba sun kuma nuna cewa an samu rahotannin cin zarafin yara ta hanyar lalata guda 2,141, yayin da yara 2,093 suka fuskanci tilasta musu aure.
Haka kuma, hukumar ta samu rahotannin hana yara 2,581 damar samun ilimi, da kuma fataucin yara 1,681 a cikin watan.
Ojukwu ya ce waɗannan alƙaluma na nuna girman matsalolin da mata da yara ke fuskanta, tare da nuna buƙatar ƙarfafa matakan kariya da tabbatar da cewa ana hukunta waɗanda suka aikata laifukan.
Ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka na tauye muhimman haƙƙoƙin ɗan Adam, ciki har da haƙƙin rayuwa, mutunci, daidaito, ’yanci daga wariya da kuma kariya daga cin zarafi da amfani da mutum ta hanyar da ba ta dace ba.
Shugaban hukumar ya ce ya zama wajibi a haɗa kai wajen magance munanan al’adu da ɗabi’u da ke ƙarfafa cin zarafi, wariya da tauye haƙƙin mata da yara.
Ya yi kira da a ƙarfafa hukumomin da ke da alhakin kare waɗanda aka zalunta, tare da tabbatar da cewa suna samun damar kai ƙara ba tare da fargabar tsangwama ko ƙarin cin zarafi ba.
Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta haɗa gwiwa da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ɓangaren shari’a, ’yan majalisun dokoki, makarantu, cibiyoyin lafiya, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula domin inganta hanyoyin dakile cin zarafi da taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
Ojukwu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi watsi da munanan al’adu, zargin waɗanda aka zalunta da kuma duk wani nau’in wariya da ke hana mutane samun kariya.
Ya ce ya kamata a samar da yanayin da mata da yara za su iya kai rahoton cin zarafin da suka fuskanta ba tare da tsoron wulaƙanci ko nuna musu wariya ba.
Hukumar ta jaddada cewa babban burin gangamin shi ne tabbatar da cewa waɗanda aka zalunta sun samu kariya da adalci, yayin da masu aikata laifuka ke fuskantar hukuncin da ya dace.
