Zaɓen Gwamnoni: APC ta lallasa PDP a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

A ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen Gwamna da na ‘yan majalisun dokoki, wanda malamar zaɓe a rumfa mai lamba 001 dake cikin Makaranar Firamaren Katuzu, a Gashuwa ta jihar Yobe ta jagoranta, Shugaban Majisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya lashe mazaɓarsa da tazara mai yawa a zaɓen.

Da take bayyana sakamakon, jami’ar zaɓen, Malama Rahama Ahmad ta ce ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar APC shi ne ya samu gagarumar nasara a rumfar zaɓen da yawan ƙuri’a 435 yayin da abokin takararsa na PDP ya samu ƙuri’a 295.