A daina nuna wariya ga masu nakasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Aminu (ba asalin sunansa ba ne), wani yaro ne mai kimanin shekaru takwas zuwa goma wanda Allah ya ƙaddarawa samun nakasa ta shanyewar kafafu tun yana ƙarami, wata majiya ta shaida min cewa cutar shan inna ce wato polio ta nakasa shi.

Duk da kasancewar ya taso a gaban iyayensa kuma cikin babban gari ba ƙauye ba, amma na lura da yadda iyayensa kan fito da shi ƙofar gida yana bara.

Duk lokacin da na fito da safe zan tafi aiki ta nan qofar gidansu nake wucewa. Mai yiwuwa ganin yadda nake kulawa da abubuwansa, ya sa shi ma da zarar ya hango ni zai fara fara’a yana ɗaga min hannu, don na tsaya a wajensa. Ni kuma saboda sabo, ba na mantawa da shi, ko da kuwa lokacin da nake wucewa bai fito ba ko kuma ya shiga gida.

Allah ya sani ba na jin daɗin yadda nake ganin wannan ƙaramin yaro da ke cikin gatansa ake ƙoƙarin ɗora shi a hanyar bara ko roƙo, alhalin sauran ’yan uwansa suna gida ko makaranta. Sai da ta kai ga wata rana na yi wa wani daga cikin maƙwaftan iyayen yaron magana, wanda na san idan ya yi magana za a saurare shi, don a daina sa yaron nan bara, kuma a saka shi a makaranta kamar sauran ’yan uwansa. Kafin daga bisani wata rana na zo wucewa kamar yadda na saba, sai na gan shi cikin rigar makaranta.

Ko da ya ke an sa shi a makaranta, amma duk da haka bai daina zama yin bara da gaishe da masu wucewa ba, don ya samu wanda zai ba shi sadaka ko ya yi masa wani alheri.

Abin baƙin cikin ma a ‘yan shekarun sa ba shi da wani wayon ajiye kuɗi ko ya tara don yin wani abin kirki da zai taimaki rayuwarsa da shi, sai dai su iyayensu yi amfani da abin da ya ke samu su yi cefane ko kashe wata wutar gaban su!

Abin da ya sa ni wannan doguwar shimfiɗa da labarin wannan yaro Aminu, wanda a lokacin yin wannan rubutu ina kyautata zaton ya girma har ma ya zama saurayi, shi ne yadda ake nuna ƙyama ko wariya ga masu nakasa.

Ana ganin su kamar ba mutane ba, ko wasu abin wulaƙantarwa, saboda ba sa iya yin komai kamar kowa. Dubi dai wannan yaron da ya kamata a ce iyayensa sun ba shi kulawa sosai, kuma ba su nuna masa bambanci kamar sauran yaran da suka haifa ba. Amma sun mayar da rayuwarsa ta zama musu kamar jari, yana nemo musu kuɗin cefane, kamar rayuwarsa ba ta da wani amfani a wajensu, saboda ya samu nakasa. Sai ka ce ba sakacin su ne ya jawo masa ba.

Na san wasu kuma za su iya cewa ƙaddarar ubangiji ce. E, na yarda. Amma haqqin iyayensa ne su ba shi kyakkyawar rayuwa, wacce ba zai ji shi daban ne a cikin sauran yara ba.

Sai dai ba haka labarin yake ba, a ɓangaren Ahmad wani abokina da muka taso tare tun muna ƙanana, wanda shi ma Allah ya jarabce shi da nakasa a ɗaya daga cikin ƙafafunsa a dalilin kuskuren jinya, inda wani ma’aikacin lafiya da ba ƙwararre ba ya yi masa allura ba a daidai ba, kuma a dalilin haka ya samu shanyewar ƙafa, da ta yi sanadiyyar gurguncewarsa.

Iyayen Ahmad na da wayewa kan muhimmancin ilimi da rayuwa, don haka ba su yarda sun wofintar da rayuwar yaronsu ba, ko sun jefar da shi a titi yana bara ba. Ahmad ya samu kyakkyawar kulawa da tarbiyya, ya kuma yi karatu tun daga firamare har zuwa digiri, yanzu haka ma babban ma’aikaci a wata ma’aikata ta Gwamnatin Tarayya.

Yana rayuwa cikin mutunci da rufin asiri, kuma mutane na mu’amala da shi cikin girmamawa ba tare da la’akari da nakasar da ya ke da ita ba. Akwai ire irensa maza da mata da ke rayuwa cikin mutunci, duk kuwa da nakasar da ubangiji ya jarabci rayuwarsu da ita.

Sau da dama za ka ga yara irin haka da za su taso a dalilin wata nakasa da suka samu a wata gava ta jikin su, sai ka ga ba a iya jan su a jiki kamar sauran yara, ko ba a damuwa da sanya su a makaranta ko wata sana’a da za su samu abin dogaro a rayuwar su. Sai a riqa ganin ai ba sauran abin da ya dace da su sai bara. Duk kuwa da ƙoƙarin da hukumomi ke yi na faɗakarwa a kafafen watsa labarai, ana dakushe zukatan masu nakasa da ma waɗanda suka ɗauki bara a matsayin sana’a cewa, nakasa ba kasawa ba ce.

Har ma da ƙoƙarin da na ga wasu ƙungiyoyi irin na kurame suna yi wajen sa ido don hana masu fakewa da kurumta suna bara a kasuwanni, tashoshin mota da wuraren taruwar jama’a.

Da wuya ka je wata ƙasa a duniya da ba za ka ga mabarata a titi ko a wasu kevantattun wurare suna bara ba, wasu don neman abin da za su ci a dalilin talauci da rashin gata, ko kuma don neman tallafin rayuwa saboda wata nakasa da ke tare da su. Duk kuwa da cewa a wasu ƙasashen gwamnatocin su na da wasu tsare tsare na tallafawa irin waɗannan mutane marasa gata da masu nakasa, da kuma kafa dokar hana bara a titi.

A wani ƙiyasi na Majalisar Ɗinkin Duniya an bayyana cewa akwai kimanin mutane Biliyan ɗaya a duniya wato kashi 15 cikin ɗari na mutanen duniya na da nakasa a wani sashi na jikinsu, sai dai ba dukkan su ne ke bara ko gararamba a titi ba, akasarin su na da rayuwar da suka dogara da ita ko ayyukan da suke yi na moriya.

Kamar yadda wata ƙididdiga ta nuna cewa a Nijeriya akwai kimanin kashi bakwai cikin ɗari na yara da shekarunsu suka wuce biyar, da kuma kashi tara cikin ɗari na manya da shekarunsu suka wuce 60 waɗanda ke rayuwa cikin ƙunci da tagayyara saboda wata nakasa da suke fama da ita.

Ko da yake a shekarar 2018 gwamnatin Nijeriya ta kafa wata doka da ta haramta nuna wa nakasassu, masu buƙata ta musamman, wariya da ƙyama, amma duk da haka ba ta canja zani ba. A mu’amala ta yau da gobe, a makarantu da wuraren ayyuka, wani lokaci har ma a wuraren ibada. Akwai wasu abubuwa da dama da ake ganin bai dace a ga mai nakasa a wajen ba, ko kuma shi matsayin sa bai dace da wajen ba!

Ƙoƙarin da Gwamnonin wasu jihohi suka yi na kafa hukumomin kula da haƙƙoƙin nakasassu da sanya wasu masu iliminsu cikin harkokin gwamnati, ya taimaka wajen ɗaga darajar su da ƙara ba su bakin magana, a inda suka ga ana nuna musu wariya da bambanci. Ko da ya ke wasu daga cikin mambobin waɗannan hukumomi na kokawa da rashin ba su muhimmancin da ya kamata daga ɓangaren gwamnati.

Na so in ji daga bakin Babban Sakataren Hukumar Kula da Nakasassu ta Ƙasa, James Lalu, dangane da abin da hukumar sa ke yi wajen isar da koke koken masu buƙata ta musamman da a lokuta da dama suke ƙorafin ana hana musu damar cin wata moriya ta gwamnati a matsayin su na ‘yan ƙasa, duk da ilimi ko cancantar da suke da ita. Amma har kawo lokacin haɗa wannan rubutu bai waiwayi saƙona ba, duk kuwa da amsa min da ya yi na cewa ya ga saƙona.

Muhammad Hussaini Yakubu, wani matashi ne ɗan asalin Jihar Bauchi daga Ƙaramar Hukumar Toro, wanda ke shekarar ƙarshe ta karatun nazarin aikin jarida a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Tun a shekarar 2015 ya gamu da lalurar makanta, yana shekara ta uku a sashin nazarin lafiyar dabbobi da ke Tsangayar Nazarin Harkokin Lafiya ta Jami’ar Ahmadu Bello, wanda hakan ya tilasta masa canja sashin da ya ke karatu, saboda yanayin da ya samu kansa a ciki ba zai yiwu masa zama cikakken likitan dabbobi da makanta ba.

Labarin Muhammad labari ne mai cike da ban tausayi da takaici a wani ɓangaren, saboda yadda rayuwa ta canza masa, a matsayin sa na matashi mai cike da burika da yawa, da fatan ganin ya gina kyakkyawar rayuwa. A yayin da ya ke da lafiyarsa yana kan cigaba da karatu a sashin nazarin cututtukan dabbobi, Gwamnatin Jihar Bauchi a lokacin Gwamna Isa Yuguda, ta ba shi aiki na wucin gadi da shi da sauran abokan karatun sa da ke Tsangayar Nazarin Harkokin Lafiya, tare da alƙawarin idan sun kammala karatunsu za a tabbatar musu da aikin su.

Amma kafin nan gwamnatin Bauchi ta riƙa biyansu wani alawus duk wata, wanda da shi ne Muhammad Hussaini Yakubu da aka tura shi ƙarƙashin Ma’aikatar Gona da Raya Karkara, ya riqa biyan kuɗin makarantarsa da sauran buƙatun karatu.

Sai dai kash, a sakamakon lalurar da ya samu kansa a ciki, wacce ta yi sanadiyyar canja vangaren karatun da ya ke yi, zuwa sashin nazarin aikin jarida, sai Gwamnatin Jihar Bauchi ta janye takardar aikin wucin gadi da ta ba shi da dakatar da alawus ɗin da ta ke biyansa. Wannan dalili ne ya sake jefa rayuwar Muhammad cikin wani mawuyacin hali. Biyan kuɗin makaranta ya gagara, karatu ya fara fuskantar tangarɗa.

Yayin aikin tantance ma’aikata da Gwamna Abdulƙadir Bala Muhammad ya sanya aka yi, a farkon zuwansa, kwamitin da aka ɗorawa alhakin gudanar da aikin tantancewar ya bayyana wa Muhammad cewa, ba ya cikin ma’aikatan gwamnatin Jihar Bauchi, don haka idan yana da wani ƙorafi ya je ya samu Gwamnan Jihar Bauchi, ko wani da zai taimaka masa.

Wannan mataki na kwamitin ya sake jefa rayuwar Muhammad cikin garari, domin kuwa babu irin jelen da bai yi ba, tsakanin ofishin Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Abdulkadir Bala Mohammed, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, da Hukumar kula da Harkokin Nakasassu ta Jihar Bauchi, duk da halin makanta da ya ke ciki.

Har kawo lokacin wannan rubutu, Muhammad Hussaini Yakubu bai san makomarsa ba, ga shi yana daf da kammala karatunsa da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, in ban da yajin aikin ASUU da ya dakatar da harkokin karatu tsawon watanni takwas ɗalibai na gida. Ba Muhammad kaɗai ba, akwai ire iren sa da dama da ke ganin an hana musu wata damar karatu ko aiki da sauran haƙƙoƙin da kowanne ɗan ƙasa ya ke samu, saboda nakasar da ke tare da su ko wata lalura ta ciwo.

Muna kira ga hukumomin da kula da walwalar nakasassu, iyayen yara masu nakasa ya shafa, su riqa kula da haƙƙoƙin masu nakasa bisa dokokin ƙasa da na Majalisar Ɗinkin Duniya, a riqa tausayawa masu nakasa da makomar rayuwar su. Haka kuma hukumomi su riqa bibiyar abubuwan da ke faruwa, don tabbatar da ganin an yi wa kowa adalci.