A guji amfani da maganin ‘B-GAG’ – Hukumar NAFDAC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da dokar abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta yi kira ga ƴan Najeriya da su guji saya ko amfani da wani magani mai suna ‘B-GAG’ na ruwa, sakamakon shiga kasuwa da ya yi ba tare da cike ƙa’idoji ko yin rijista da hukumar ba.

Bayanin ya fito ne daga ofishin darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye a wata takardar sanarwa mai lamba 023/2024 a ranar Lahadin da ta gabata inda ta ce, ana sayar maganin wanda ba a tantance ko yi masa rijista ba daga wani kamfani mai suna ‘Babban Gida Agalawa General Enterprises’ da ke da adireshi kamar haka; ‘No. 883/884 Western Bypass Ring Road, Kumbotso Local Government, Kano State’.

Kamar yadda jawabin ya nuna, samfurin maganin shi ne a irin ƙaramin kwalaben magunguna na ruwa yake, sannan bashi da lambar NAFDAC.

Ta kuma ce, an gano hakan ne a yayin wani atsayen bincike a ɓangaren kasuwanci da wakilan hukumar reshen Jihohin Barno da Nassarawa da suka yi a Maiduguri da Keffi inda ta ce matuƙar bata tantance tare da bada lasisi ga sayar da magani ba, to zai iya zama barazana ga lafiya, don haka al’umma su guji amfani da ire-iren waɗannan magunguna.

Leave a Reply