A karon farko tuɓaɓɓen sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya magantu

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya koka da yadda ya baiwa jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya Amana, amma suka ci amanarsa.

“Alhamdulillah na gama aiki lafiya, amma dai Allah ya haɗa mu da mutane marasa amana, mun ba da gudunmawa daidai gwargwado, amma an ci amanarmu. Ina baku haƙuri ku jira lokaci zai yi da zamu fito da maganganu sala-sala”.

Dakta Baffa Bichi ya bayyana hakan ne lokacin da wasu matasa maza da mata suka taro shi bayan ya dawo daga ƙasa mai tsarki domin gudanar da ibadar Umara.

Kazalika ya ce yanzu ba lokacin magana ba ne, amma idan lokacin yayi matasan za su ji bayanai kala-kala.

” Na gode muku, ina kuma ba ku haƙuri, yanzu ba lokacin magana ba ne, amma muna da maganganu a rubuce muna da su a sauti da bidiyo idan lokacin ya yi za mu fito da su sala-sala”. Inji Baffa Bichi

Dakta Baffa Bichi dai ya ce zai fito ya faɗawa duniya rashin amanar da aka yi masa don gudun kada a ƙara basu amana, inda ya kira su da masu faɗar amana a baki amma kuma ba su da ita a aikace.

Idan za a iya tuna dai Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Dakta Baffa Bichi na cikin waɗanda gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauke daga muƙaminsa na Sakataren gwamnati a cikin shekarar 2024.

By ukarofi