A karon farko za a fara gasar daddalla mari a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu shirya wata sabuwar gasa da za a fara a karon farko a Nijeriya, sun ce a fito a fafata domin za a fara gasar mare-mare cikin watan Oktoba a Nijeriya.

Babban Daraktan kamfanin tsara wasannin na TKK Sports, Abdulrahman Orosanya ne ya bayyana haka, ranar Juma’a a Legas.

Ya ƙara da cewa, ba a dai sa ranar da za a fara ba, amma dai cikin watan Oktoba za a fara, kuma a cikin Disamba za a yi wasannin ƙarshe na cin kofuka.

Orosanya ya ce, an ƙirƙiro wannan wasan daddalla mari a ƙasar Rasha, amma ƙasar Amurika da qasashen Turai su ka zamanantar da shi.

“A yanzu ana gudanar da wannan gasa a Rasha, Amurka, Burtaniya, Poland da Afrika ta Kudu. Za a tsara gasar mataki-mataki. Akwai matakin ramammu, tsaka-tsakiya, ƙarti, sai kuma na jibga-jibgan ƙarti.”

“A ƙa’ida ba za a kantsama wa abokin gasa mari a cikin ido ba, kuma ba za a mari mutum a muƙa-muƙi ko a kan kunne ba. Kumatu kaxai za a riƙa falla wa mari da tafin hannu.

Ana yin galaba ne idan an gaura wa mutum mari ya kife ƙasa ko ya nuna an fi ƙarfinsa. Inda gwanaye biyu su ka nuna dauriya da jarunta kuwa, to alƙalin wasa ne zai yanke hukunci.

“Za a horas da ‘yan takarar gasar da alƙalai kafin lokacin fara gasar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *