Hidimar da Charles Henry Robinson ya yi wa harshen Hausa

Duk ƙasar da ta ke son mallakar ƙwaryar Afrika, dole sai ta mallaki Bahaushe – Mista Johnson

Daga JAAFAR JAAFAR 

Shekaru 130 da su ka gabata, a ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 1891, John Alfred Robinson, wani Bature malami a Christ’s College ta Cambridge, ya mutu a garin Lokoja. Wannan Bature, wanda ya fahimci Hausa daidai gwargwado, ya na cikin mutanen da su ka fara fahimtar amfanin nazarin harshen Hausa.

Watanni kaɗan bayan rasuwar wannan Bature, sai wasu Turawa su ka haɗu a wani otal da ya ke a Birnin London mai suna Charing Cross Hotel don tattauna yadda za a ci gaba da aikin da John ya fara a kan harshen Hausa don “fara nazarin yaren a doron kimiyya da fassara littattafan addini da wasu littattafai masu amfani, don ƙaruwar Bahaushe.”

Turawan da su ka haɗa wannan qungiya ta Hausa sun haɗa da Farfesa Max Müller da Farfesa Peile da Farfesa Margoliouth da Farfesa Robertson Smith.

Sauran sun haɗa da Mista MacGregor Laird da Mista Francis Galton da Mista FRS da Manjo Darwin da wakilin hukumar ‘West African Enterprise’ kuma gwamnan ‘Royal Niger Company’, wato Lord Abedare, da kuma mataimakin sa, Sa George Taubman Goldie.

Waɗannan Turawa sun yi shawarar nemo mutumin da zai tafi Ƙasar Hausa ya yi cuɗanya da Hausawa, kuma ya nazarci yaren su da al’adun su.

Bayan an yi shekara ana shela a jaridu da mujallu na ƙasar Birtaniya, kwamitin ya samu takardu daga waɗanda ke sha’awar wannan aiki. Amma sai dai duk waɗanda su ka nema, ba su samu cancantar da kwamitin ke buƙata ba.

A ranar Asabar, 5 ga Nuwamba, 1892, wasiƙa ta iske Charles Henry Robinson ya na kan aiki a garin Truro na shiyyar Cornwall da ke ƙasar Ingila, cewa ana neman amincewar a saka sunan sa a cikin waɗanda za a tantance a matsayin ɗalibin Hausa (Hausa studentship).

Bayan da Robinson ya yi nazarin wasiƙar, sai ya ga cewa ya dace da ya ƙarasa aikin da ɗan’uwan sa ya fara. Shi Charles ƙane ne ga John, wancan Bature da ya rasu a Lokoja.
Bayan kwamitin ya tattauna da shi don tabbatar da dacewar sa, daga bisani aka tabbatar da shi a matsayin ɗalibin Hausa na farko.

Ƙa’idojin aikin sun haɗa da fara zuwa Kano da wasu manyan garuruwan ƙasar Hausa, amma saboda yanayin rashin sabo da yanayin ƙasar Hausa, sai aka bada shawarar ya fara zuwa birnin Tarabulus (Tripoli kenan) na ƙasar Libiya ko birnin Tunis na Tunisiya don fara koyon Hausa da Larabci a can, daga bisani sai ya zarce ƙasar Hausa.

A ranar Lahadi, 30 ga Afrilu, 1893 ya baro ƙasar Ingila zuwa birnin Tarabulus, ya isa cikin kwana 40.
A wancan zamanin, akwai kimanin mutane 36,000 a birnin Tarabulus, kuma daga cikin su akwai kimanin mutane 600 da ke jin yaren Hausa. A cewar Robinson, akasarin masu jin Hausar sun zo ne a matsayin bayi ko barori, kana kuma akwai mahajjata da hanya ta biyo da su, su ka yada zango. Ya ce akwai dubunnan maniyyata aikin Haji daga ƙasar Hausa da ke yada zango a wannan gari kafin su wuce garin Suakin da ke Sudan don tsallaka tekun Maliya zuwa Jiddah.

Cuɗanyar Robinson da irin waɗannan maniyyata ta sa ya fara koyon harshen Hausa. Amma bayan ya yi wata shida a birnin Tarabulus, sai ya fahimci cewa ratsa Sahara don zuwa ƙasar Hausa ba abu ne mai sauƙi ba.

Garin Tarabulus a lokacin ya na ƙarƙashin daular Turkiyya, kuma Pasha (gwamnan garin) ya karɓi ‘oda’ daga babban birnin daular, wato Kwasɗanɗinu (wanda a yanzu ake kira Istanbul) da kada ya bari Turawa su wuce mil 10 daga garin. Dalili kuwa shi ne ƙabilun da ke kan hanyar, musamman Abzinawa, su na far wa Turawa.

Da Robinson ya fahimci tarnaƙin keta Sahara ta birnin Tarabulus zuwa ƙasar Hausa, sai ya tafi birnin Tunis don gwadawa ta can.

Saukar sa ke da wuya a garin Gabes tare da shi da Mista Harris, sai ya sayi raƙuma guda biyu. Haka ya yi sati uku ya na zarya a wata hamada da ke tsakanin kudancin birnin Tunis da Aljas.

Bayan da ya gama rangadin, sai ya dawo Tunis. Daga nan ne sai ya koma Ingila ya yi wata shida ya na koyon aikin likitanci (don shirya wa zuwa qasar Hausa), kana kuma ya halarci tarurruka na ‘Hausa Association’ da aka kira.

Robinson ya sake komawa dai birnin Tunis inda su ka yi tsawon wata shida tare da shi da Dakta TJ Tonkin (abokin tafiyar sa zuwa Kano), su na koyon Hausa da Larabci.

Da su ka sake fahimtar cewa tsallaka Sahara abu ne mai tsananin wuya, a watan Yunin shekarar 1894, sai su ka sake dawowa Ingila don zuwa ƙasar Hausa ta teku, zuwa Kogin Kwara. Dab da barin Tarabulus, Robinson ya ƙara samun abokin tafiya, wato Mista John Bonner, wanda ya koyi Larabci a dalilin zaman sa na shekara biyu a Tarabulus.

Da ya koma Ingila, an yi taro sau biyu na ‘Hausa Association’. An fara yin taron a ranar Talata, 3 ga Yuli a ɗakin taro na Majalisar Kasuwanci ta London (London Chamber of Commerce). Taron, wanda Sa A. Rollit ya jagoranta, ya samu bayanai daga Mista HH Johnson da Mista HM Stanley waɗanda su ka bada bayanai a kan haɗuwar su da Hausawa.

Mista Johnson ya ce: “A yawace-yawacen da na yi a ƙasashen Afrika, na fi haɗuwa da Bahaushe a kan kowace ƙabila, kuma harshen Hausa ya fi kowane yare yaɗuwa a arewacin Afrika. Saboda haka, duk kuwa ƙasar da ta ke son mallakar ƙwaryar Afrika (Central Soudan), to kuwa dole sai ta mallaki Bahaushe… Ina fatan wata rana za a samu farfesoshi a jami’un mu na fannin Hausa da Suwahili.”

Shi kuwa Mista Stanley, ya yi magana ne a kan wani Bahaushe da ya haɗu da shi a Ƙasar Kwango. Ya ce fiƙirar Bahaushe da son littafi daban ta ke da yadda jahilci da camfe-camfe su ka yi wa ƙabilun Kwango katutu.

A taro na biyu, wanda aka yi a ranar Juma’a, 13 ga Yuli a ɗakin taro na Liverpool Town Hall, Sa George Taubman Goldie da sauran mahalarta taron sun yi jawabai.

Bayan wannan taro na biyu ne, gari na wayewa Robinson da shi da Dakta Tonkin da Mista Bonner da Salam (wani Balarabe mai hidimta masu) su ka hau jirgin ruwa mai suna ‘SS Loanda’ don zuwa gaɓar Kogin Kwara. 
(Idan na samu lokaci, zan kawo labarin zuwan Robinson Kano da haɗuwar sa da Sarkin Kano Alu da kuma yadda ya rubuta ƙamus na Hausa zuwa Turanci na farko. Na tsakuro wannan labari daga littafin CH Robinson mai suna ‘Hausaland: Or 1500 Miles Through Central Soudan’).

Malam Jaafar fitaccen ɗan jarida ne kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian