Rashin sha’awar iyali da dalilansu (4)

Daga BILKISU YUSUF ALI

Daga makon da ya gabata mu na tattaunawa ne kan sha’awa tsakanin ma’aurata da abin da yake ɗauke ta ko ya sa ta yi rauni. Daga yanda mutane suke bibiya tare da yin tambayoyi wannan ya nuna rashin sha’awa wata gagarumar matsala ce da ta addabi al’ummarmu.

Kamar yadda muka fa]a a baya yau za mu kawo hanyoyin magance wannan matsalar a mataki na farko kafin mataki na gaba na shan magani.

Sakewa:
Yana da kyau yayin kusantar juna ma’aurata su sake da junansu sakewar gaske. Ya kasance sun mallakawa junansu kawunansu tsakaninsu ba tsoro ko shayi ko kunya ta haka ne za su gane mai suke buƙata don tabbatar da wannan sha’awa. Don haka dole a sallamawa abokin zama zuciya da gangar jiki. Sannan a cire duk wani abu da ke cikin zuciya na damuwa ko wata matsala a tabbatar ba komai a zuciya da kwakwalwa sai ƙaunar juna da wannan buƙata da aka saka a gaba.

Muhalli:
Idan har ana son a samu sha’awa sai an gyara muhalli an kawar da duk abin da yake zai kawo cikas. Misali tsafta an gyara ko’ina an sa abu mai kamshi dai-dai gwargwado an ƙawata wajen , yanayin tsafta da ƙamshi kan sa a samu shauƙi da sakin jiki. Wasu za su yi tunanin su ce to ina ga masu fyaɗe ko masu kusantar mace a bola ko kan hanya ko wani waje marar tsafta? To wannan daban. Wannan yana faruwa haka ne da taimakon shai]an da kuma neman biyan buƙata don wani dalili. Tsaftar jiki ga ma’aurata musamman mace yana da muhimmanci saboda mace ita za ta janyo sha’awa kada ki yi la’akari da wai an zama ɗaya ko an jima. In har kina son ki jawo sha’awar Maigida sai kin dage da tsafta da kwalliya da turare da tsaftar baki da jiki inda da ya doso ki ba abin da zai gani ko ya ji wanda za su sosa masa rai.

Hutu:
Idan har babu kyakkyawan hutu da bacci mai kyau musamman aƙalla wanda aka saba awa shida zuwa bakwai a kullum da wuya a samu kyakkyawan sakamakon da ake buƙata. Don haka ana son a samu hutu jiki ya kasance babu gajiya , don gajiya tana hana samun kyakkyawan sakamako akan sha’awa. Saboda sha’awa da kwakwalwa suna tafiya ne tare da juna. Don haka hutu yana da muhimmanci.

Zaɓin lokacin kwanciya:
Nutsuwa da samun kyakkyawan muhalli yana taimakawa wajen samun sha’awa mai ɗorewa. Ma’aurata ya kamata su san wane lokaci ne ya fi dacewa su kasance tare kuma wane lokaci ne suka fi samun nutsuwa musamman in har sun kasance suna da iyali. Wasu kan gwada farkon dare wani tsakiyar dare wani ƙarshen dare wani sai bayan asuba wasu ma sukan ɗauki rana. Ya dai dace da son zuciyar ma’aurata. Don haka yana da muhimmanci su zaɓi dacewa da lokaci saboda ana buƙatar nutsuwa.

Ga mai neman ƙarin bayani ko tambaya kan wani abu da ya shafi lafiyar iyali yana iya aiko da tambayarsa ta hanyar wannan lambar 08039475191 ko ta Page ɗina, Ilham Special care and Treatment.