Aikin MC ilimi ne mai zaman kansa a aikin jarida – MC Bahaushe

Daga UMAR GARBA, a Katsina

Kabir Sa’idu Bahaushe matashi ne da ya yi fice a fannoni daban daban, kama daga mai shiryawa da gabatar da shirye shirye a gidan radiyo, da kuma yin sharhi da rubuce-rubuce a jaridu da mujallu. Haka nan ma Kabir Sa’idu Bahaushe ya yi fice a harkar gabatar da tarurruka a gidan biki ko taron ƙungiyoyi ko kuma taron marubuta ko na mawaƙa gami da taron siyasa. Manhaja ta tattauna da Bahaushe a kan batutuwan da su ka shafi aikin shi na gabatar da tarurruka watau MC da alaƙarsa da marubuta da ƙungiyoyi har ma da alaƙarsa da ‘yan fim da kuma ƙalubalen da ya fuskanta gami da nasarori da ya samu a rayuwarsa.

Za mu so jin taƙaitaccen tarihinka?
Alhamdulillah! Sunana Kabir Sa’idu Ɗanɗagoro amma an fi sanina da MC Bahaushe, an haife ni a garin Ɗanɗagoro a shekarar 1991 na yi firamare a Ɗanɗagoro ‘Model Primary School’ na kammala a shekarar 2002 daga nan sai na tafi Makarantar sakataren GRBSS da ke Ɓatagarawa inda na kammala a shekarar 2008 na kuma nemi ilimin addinin Musulunci inda na halarci makarantar allo da Islamiyoyi na wani ɗan lokaci,daga nan kuma na sami damar shiga Jamia’ar Umaru Musa ‘Yar’adua dake Katsina inda na yi digiri na farko a ɓangaren koyarwa a fannin harshen Hausa na kammala a shekarar 2016 daga nan kuma sai na ci gaba da karatun digiri na biyu akan adabin harshen Hausa kusan saura shekara ɗaya na kammala.
Ina aiki a gidan radiyon Vision FM Katsina a matsayin mai shiryawa tare da gabatar da shirye-shirye, kuma ni ne wakilin Mujallar Arewa ne a Katsina, haka nan ma ni ne shugaban ƙungiyar Kakaki ‘Unique award’ ina kuma sana’ar mai gabatar da tarurruka watau MC ko kuma sanqiran Zamani da hHausa.

Me ake nufi da MC?
MC ya na nufin Master of ceremony a Turance ke nan, ko kuma a hausance a ce sanƙirar zamani amma dai a taƙaice MC ya na nufin mai gabatar da taro shine wanda ya ke magana lokacin da za a fara taro,mai gabatar da wanda zai yi magana a lokacin gudanar da taro, kuma shine wanda ya ke bada damar a shaƙata a wurin taro kuma shine mai rufe taro.

MC ilimi ne mai zaman kanshi vangare ne daga cikin aikin jarida, za ka ga a ma’aikatun gwamnati ma akwai PRO sune ma su gabatarwa a ma’aikatun su, saboda muhimmancin shi yanzu akwai makarantu da ke koyar da harkar MC misali akwai ‘PR academy’ da ke Abuja dole sai ka na da ilimin shi saboda za ka tsaya a gaban manyan mutane kamar Sarki, gwamna, minista, sanata ko wani babban attajiri don ka gabatar da mahallartan taro a gaban waɗannan manyan mutane.

Waɗanne wurare aikin MC ya kai ka?
Ba zan iya faɗar wuraren ba duka saboda a koda yaushe ana kan gayyata ta amma a taƙaice na je Kano, Jigawa, Kaduna, Abuja, Neja, Mai duguri, Zamfara da kusan dukkan ƙananan hukumomin Katsina da kuma Ƙasar Nijar, ina alfarin kasancewar ni ne matashin da ke amfani da kalmar MC a sunan shi saboda nasarorin da muke samu a aikin wasu matasan har sun fara kiran kan su da MC duk da cewa wasu suna amfani da sunan ne kawai amma su ɗin ba MC ba ne.

Shin akwai wanda ka koyi aikin MC a wurin shi?
Zan kasa tambayar biyu idan daga nan gida ne (Katsina) wanda na fara ganin ya na harkar MC kuma abun ya burge ni har na ji ina son na shiga harkar shine DJ Amo da kuma Rabi’u M. Yaro bayan tafiya ta yi tafiya Allah ya ɗaga ni na ƙware a harkar sai abokina Isa Bawa Doro ya haɗa ni da ‘MC big boy’ wanda ke Kaduna, shi kuma shakurukundum ne a harkar saboda shi ne ya yi MC a lokacin bikin ɗiyar shugaba Buhari watau Zahra Buhari. A gaskiya ya na bani shawarwari kuma ina samun ilimi a wurin shi shiyasa ni yanzu idan wani ya ce mani MC ɗin gidan biki za mu yi dambe da shi sai dai ka ce mun MC mai gabatar da taron biki ko suna, taron marubuta ko kamfani ko na siyasa saboda ba MC ɗin taron biki kaɗai ya ke gabatarwa ba, shi kuma biki ba koda yaushe ake yin shi ba.

Wane shirye-shirye ka ke yi don ganin ka haɓɓaka sanarka ta MC?
Ina da ƙudurori guda uku na ganin na kafa wata ƙungiya ta ma su harkar MC a Arewa, amma alhamdu lillahi an kafa wata qungiya ta masu harkar MC wadda aka ba mai gidana ‘MC big boy’ jagorancin ta, na biyu ina son buɗe babban ofishina na musamman na uku shine wanda ya fi muhimmanci saboda za mu kira masana su ilimanatar da ma su sana’ar wanda shine babban shirin da nake yi don havaka sana’ar.

Me nene alaƙarka da ‘yan fim?
Kasan matasa na tashi da sha’awar fasaha, akwai abokina Isa Bawa Doro da zance ya na ɗaya daga cikin waɗanda suke sha’awar harkar finafinai a lokacin shine wakilin Mujallar Fim, ni kuma wakilin Mujallar Arewa, sakamakon haka mu kan yi hira da manyan ‘yan Fim irin su Ali nuhu, Umar M shariff da sauran su, to haka muka san juna, yanzu shi Isa mai shirya finafinai ne ni kuma ina gabatar da tarurrukan da su ka haɗa da jaruman Finafinan hausa da kuma harkar Fim.

Ka taɓa fitowa a Fim?
Na taɓa fitowa a wani fim mai suna ‘Ɗaurin Zato’ na marigayiya Binta Ƙofar Soro duk da dai ni ba cikakken jarumi ba ne, amma ina da kyakkyawar alaƙa da su Saboda ko a shafina na Instagram za ka ga manyan jaruman finafinan Hausa suna bina, kuma suna saka hotunana a shafukan su na sada zumunta, haka ma idan za a yi taron bada kyaututtuka musamman a Katsina watau ‘award’ na kan jagoranci taron, koda a lokacin da aka yi taron bada ‘award’ na AMA nine na jagoranci taron ta haka muka san juna da ‘yan fim kuma muka ƙulla alaƙa.

Ko Kana da alaƙa da nungiyoyi?
Ina da alaƙa da ƙungiyoyi saboda ni ne shugaban ƙungiyar Kakaki Unique award ƙungiya ce mai zaman kanta kuma mai rijista an kafa ƙungiyar ne don inganta kasuwanci da tallace tallacen gwamnati a kafafen yaɗa labarai, haka nan ƙungiyar tana karrama mutane daban-daban da su ka yi nasara a rayuwa, bayan nan ina gabatar da wani shiri mai suna ‘Duniyar Matasa’ a gidan radiyon Vision FM Katsina, shirin ya kan tattauna da ƙungiyoyi ma su rijista saboda haka na san ƙungiyoyi da NGOs daban-daban don haka kaga ina da alaƙa mai ƙarfi tsakani na da su.

An ce kai marubuci ne. Shin haka abun yake?
Ba zan ce ni ba marubuci bane, amma gaskiya ba marubucin littafi bane, sai dai ina rubutu mai tsawo da sharhi a jaridu da mujallu koda yake ina son na rubuta littattafai amma ba na soyayya ba, littattafan ilimi Saboda duk wanda ya sanni ya san cewar ba a raba ni da littattafai iri iri na Hausa dana Turanci.

A ganinka ta wace hanya ne mutane su ka fi saninka tsakanin gidan radiyo da kuma soshiyal midiya?
A Katsina an fi sanina da aikin gidan radiyo da kuma sana’ata ta MC saboda yadda ake jin muryata kusan koda yaushe, sai dai a sauran jihohin Arewa an fi sanina ta kafar yaɗa labaran zamani saboda ina wallafa hotunana dana aikina a shafukan soshiyal midiya don in qara tallata sana’ata, amma dukka guda biyun suna da amfani a gare ni kuma sun sa an sanni sosai.

Wace shawara za ka ba matasa akan su dage su nemi na kansu?
Matasa su tashi tsaye su nemi na kansu zama ba sana’a ba nasu bane a wannan lokacin, kowa ya cire girman kai ya nemi aiki ko sana’a, kuma mu dinga haɗa aiki biyu ko uku muna yi saboda idan ba wannan to ga wancan.

Wane ƙalubale ka fuskanta kafin ka taka matsayin da kake a kai yanzu?
Duk wanda ya sanni ya sanni da naci duk girman ƙalubale ina ɗauke shi in wuce, an ɗan fuskanci ƙalubale amma babban ƙalubalen bai wuce a lokacin da nike gabatar da taro ba sai kaga wani ya zo wanda ba bu sunan shi a cikin wanda za su yi magana ko waƙa amma sai ya ce dole sai an bashi dama ya yi ko kuma a ce ma mutane su zauna ko su yi saurara amma su ƙi yin abunda aka umarce su, ko kaga suna wawar abinci wannan shine ɗan ƙalubalen kawai shima Saboda an saba bai fiye damuna ba saboda mu na yin amfani da wa su dabaru don dai daita wurin.

Waɗanne nasarori ka samu a rayuwarka?
Na samu nasarori da dama, na samu kyaututtuka irin su mota, kujerar aikin hajji, wayoyin salula, na yi aure cikin ikon Allah na haɗu da manyan mutane kuma na je wurin da ban taɓa tsammanin zan je ba sai a dalilin aikace aikace na wannan duk nasarori ne.

Mun gode sosai MC Bahaushe.
Ni ma na gode da ziyarar Manhaja don tattaunawa da ni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *