A nemi watan Shawwal ranar Talata, in ji Sarkin Musulmi

Daga FATUHU MUSTAPHA

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar Musulmi na ƙasa baki ɗaya su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Talata.

Mataimakin Babban Sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu, shi ne ya sanar da hakan Asabar da ta gabata.

A cewarsa, biyo bayan shawarar Kwamitin Neman Wata na Ƙasa (NMSC), a Talata mai zuwa, wato 11 ga Mayu 2021 wanda ya yi dai da 29 ga Ramadan, 1442, a wannan rana za a nemi watan Sahawwal.

Majalisar ta ce idan Allah Ya sa aka dace da ganin wata a ranar Talata da daddare sannan ƙwararru suka shawarci Mai Martaba Sarkin Musulmi, sarkin zai ya yi wa al’umma jawabi domin bayyana Laraba, 12 ga Mayu a matsayin ranar sallah wanda hakan kuma ya zama 1 ga Shawwal kenan.

“Amma idan ba a ga wata a Talatar ba, kenan Alhamis 13 ga Mayu, ita ce 1 ga Shawwal, 1442, kuma ranar sallah”, in ji Majalisar.

Daga nan, Shehu ya yi kira ga ɗaukacin jama’ar musulmi da su sanya ido su nemi wata kamar yadda Sarkin Musulmi ya umurta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *