A yi hattara da tunkarar masu zanga-zanga

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A daidai lokacin da nake shirin fara wannan rubutu na samu kira daga wani mai bibiyar wannan shafi daga Jihar Neja, wanda ya bayyana min cewa ya karanta saƙona na makon da ya gabata, kuma shi gaskiya yana goyon bayan a ƙyale matasa su yi zanga-zangar da suke son gudanar wa, domin a cewarsa ta haka ne shugabannin ƙasar nan za su fahimci halin ƙuncin da talakan ƙasar nan ke ciki. 

Ya ce, a ƙauyen da suke a Jihar Neja kewaye suke da ’yan bindiga, waɗanda kullum cikin fafatawa suke da jami’an tsaro, kuma rayuwa ta yi matuƙar wahala a yankin. Don sai mutum ya shafe mako guda bai samu Naira ɗari ba, kuma ko ƙwadago mutum ya yi da ƙyar abin da za a biya shi zai ishe shi ya ci abinci. 

Saƙon wannan bawan Allah, wanda daga sautin muryarsa da na saurara na fahimci dattijo ne ba yaro ba. Kuma na yi imanin ba shi kaɗai ba ne mai irin wannan ra’ayi. Akwai wasu da dama da suke ganin yin wannan zanga-zanga shi ne kaɗai mafita ga halin da ake ciki, don zai ƙara zaburar da gwamnati ta ƙara ƙaimi kan matakan da ta ce tana ɗauka na rage raɗaɗin talauci. 

Tun a sharhin da na yi a makon da ya gabata na bayyana irin muhawarar da ake yi a tsakanin ‘yan ƙasa game da dacewa ko rashin dacewar yin zanga-zangar. Yayin da kawuna suka rabu biyu musamman a nan Arewa, inda wasu ke danganta abin da addini ko kuma ake ganin shawarar malamai ce ta fi dacewa a ɗauka bisa amincewa da hasashensu dake nuna akwai yiwuwar wata maƙarƙashiya ta haifar da yamutsi ko kawo lalacewar al’amura a Arewa. Kaso mafi tsoka na masu biyayya ga wannan ra’ayi sun fi ƙarfi daga almajiran waɗannan malamai, jami’an gwamnati, da ’yan kasuwa, waɗanda ke ganin idan zanga-zangar ta ɗauki zafi ana iya fasa musu wurarensu na kasuwanci. 

Amma idan mutum ya lura daga ɓangaren masu goyon bayan zanga-zangar zai ga akasari matasa ne, sai kuma ma’aikata da malaman jami’o’i ko manyan makarantu, waɗanda kullum hankalinsu ke kan irin badaƙalar da shugabanni, da ’yan siyasa suke yi, su da iyalansu cikin walwala da wadata, yayin da talakawan ƙasa ke faɗi tashin neman abin da za su sa a cikinsu, ko kuma neman kuɗin motar zuwa wajen aiki. 

Yayin da jami’an tsaro su ma a nasu ɓangaren ke jan hankalin matasa su sake tunani, kada su shiga wannan zanga-zangar da wasu ɓata-gari ke neman fakewa da ita don kawo yamutsi, da lalata dukiyar gwamnati. Mun ga rahotanni da ke nuna jami’an tsaro na shirin ko-ta-kwana don tabbatar da ganin ba a yi amfani da zanga-zangar an haifar da wani abu marar daɗi a cikin ƙasa ba. Har ma kuma a wani mataki da nake ganin an yi riga Malam masallaci, shi ne wajen kama mutanen da ake zargin suna da hannu wajen kitsa wannan zanga-zanga da ake so a yi, ko kuma suna hassala batun da neman goyon bayan mutane.

A gaskiya ina ganin yin hakan kuskure ne, duk da kasancewar ba ma hoyon bayan tayar da hankali ko yamutsi a ko ina a ƙasar nan, amma kuma ba za mu goyi bayan tauyewa ‘yan ƙasa ‘yancinsu na bayyana ra’ayinsu, sai dai a inda aka lura akwai wata maƙarƙashiya da za ta iya jefa rayukan al’umma cikin haɗari, ba don gudun kar a ƙalubalanci gwamnati ba. Haƙƙin jami’an tsaro ne su tabbatar an gudanar da zanga-zangar cikin lumana, ta yadda komai zai gudana ɗan kallo lafiya maiwasa ma lafiya. Kama masu shirin zanga-zanga ana kullewa shi ma kansa yana iya angiza wasu ko da a baya basu da niyyar shiga zanga zangar su zo su nuna su ma za su shiga, saboda nuna adawa da abinda jami’an tsaro suka yi wa abokansu.

Kwanaki biyu da suka gabata na taso daga aiki, ina motar haya tare da wasu mutane, sai muka yi kaciɓis da tawagar wasu jami’an tsaron ’yan sanda suna binciken ababen hawa. Kowacce mota ta zo sukan leƙa ciki su kalli fuskokin mutane, sannan su zaɓi wani ko wasu da suke ganin ba su amince da yanayinsu ba. Sai su fitar da su zuwa wata mota da manyansu ke ciki, su bincike su. Mu ma haka aka yi wa tamu motar, har kuma suka fitar da wani saurayi da ke zaune kusa da ni, saboda sun ganshi da gajeren wando. Sai daga baya nake fahimtar ashe bincike suke yi kan matasa masu alamar ‘yan daba ko ‘yan ƙungiyar asiri, ƙarƙashin sabuwar rundunar yaƙi da ’yan tsagera.

Wannan na zuwa ne biyo bayan rahoton asiri da ke nuna akwai yiwuwar wasu su fake da wannan zanga-zangar su haifar da damuwa a wasu jihohin ƙasar nan, ciki kuwa har da garin Jos da Kaduna. Don haka aka ƙara tsaurara matakan tsaro, yayin da jami’an Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA da rundunar ’yan sanda suke sintiri da kai samame wuraren harƙallar irin waɗannan matasa, da ake ganin da su ne za a iya amfani a haifar da rikici.

A daidai lokacin da nake aikin wannan rubutu rahotanni sun bayyana cewa akwai gungun wasu matasa daga Arewa waɗanda suka shiga cikin shirin gudanar da zanga-zanga, yanzu sun yi mi’ara koma baya, inda suka sanar da janyewarsu daga wannan shiri, sakamakon wasu abubuwa da suka bayyana musu. Jaridar Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, tsohon Shugaban Majalisar Matasa na Nijeriya, Kwamared Murtala Muhammed Garba wanda aka fi sani da Murtala Gamji, ya bayyana cewa sun gano ana so a yi amfani da zanga-zangar ne wajen shigo da wata mummunar manufa domin ruguza yankin Arewa.

Ya bayyana cewa wani jigo cikin masu shirya zanga-zangar daga kudancin ƙasar nan ya gayyaci wasu matasa su 23 zuwa wani taro a Fatakwal domin tattauna tsare-tsaren yadda za a gudanar da wannan zanga-zanga, da abubuwan da suke so a yi. A nan ne a cewarsa ya fahimci akwai wata maƙarƙashiya da ake so a shigar da ita cikin zanga-zangar saɓanin su aniyarsu ta farko kan kokawa gwamnati halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

A cewarsa, “Kalamansu tabbas sun ba mu tsoro, domin suna faɗa mana yawan sojoji da ’yan sandan da ke cikin garin Abuja da cikin Fadar Shugaban Ƙasa, suna cewa ka da mu damu za su ɗauki nauyin komai, kuma za su sa waɗansu su bi mu.” 

“Kuma hatta maganganunsu suna cusa mana ƙin jinin manyanmu da sarakunanmu da malamanmu da sauran jagororinmu na siyasa.”

Gamji ya ƙara da cewa, akwai yunƙurin shigo da wasu gurɓatattun mutane domin su dagula zanga-zangar zuwa wata manufa tasu ta daban, kamar yadda ya bada misali a Jos lokacin da aka yi zanga-zangar EndSars, inda wasu gurɓatattu suka shigo ciki aka fara ƙone-ƙone da rikicin ƙabilanci da addini.

Ko ma dai yaya take kasancewa, hakkin ‘yan sanda ne da sauran jami’an tsaro, su kasance cikin shiri da sa ido kan yadda za a gudanar da wannan zanga-zanga, kuma tabbatar an gudanar da ita cikin kwanciyar hankali. Idan zargin da aka yi na cewa akwai masu shirin tayar da fitina, lallai yana da muhimmanci a nemo inda suke a bincike su. Amma kada a ce da ƙarfin tsiya ko da bakin bindiga za a hana gudanar da zanga-zangar. Lallai mutane a kusa suke, ana fuskantar matsala sosai, kuma da alamu kiraye-kirayen basu yi tasiri sosai ba. Don haka akwai buƙatar bin hanyar lalama da wayar da kai ta kafafen watsa labarai, da kuma ɗaukar matakan da suka kamata, yadda jama’a za su yarda da gaske ana kan gyara.

By ukarofi