A zaftare albashin ‘yan majalisa a biya malaman jami’a – Sanata Ndume

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata Ali Ndume ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta zaftare albashin ‘yan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami’o’i da ke yajin aiki kudaɗensu.

Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin wani taro.

Jaridun Nijeriya sun rawaito sanatan na cewa wannan abu ne da ya shafi ƙasa bakiɗaya, kuma dole a wasu lokutan a ɗauki matakan ceto ‘yan ƙasa da ilimi.

Kiran da sanatan ya yi na zuwa ne a daida lokacin da malaman jami’i’oi ke ƙorafin cewa rabin albashinsu aka ba su bayan sun janye yajin aiki.

Ɗan majalisar dai na cewa lokaci ya yi da ya kamata a shawo kan matsalolin da ke durƙusar da fanin ilimi a Nijeriya.

A watan Oktoban da ya gabata ne, ASUU ta janye yajin aiki da ta shafe wata takwas tana yi ba tare da ta samu biyan buƙatunta daga wajen Gwamnatin Tarayya ba.