Kotun Amurka ta ɗaure ɗan damfara Hushpuppi shekaru 11 a kurkuku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun Amurka da ke gundumar tsakiyar California ta yanke wa riƙaƙƙen ɗan damfara Raymond Olarinwa Abbas hukuncin ɗaurin watanni 135 a gidan kurkuku.

Watanni 135 na daidai da shekaru 11, sannan Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, zai biya ramuwar wasu kuɗaɗe har Dala Miliyan 1,732,841 ga wasu mutum da ya damfara.

A cikin watan Afrilu 2021 ne ya amsa laifi ɗaya daga cikin laifukan da ake tuhumar sa da su. An kama shi ne a Dubai inda ya ke da zama, a cikin Yuni, 2020, kuma tun lokacin ya ke ɗaure a kurkukun Amurka, bayan kamun da aka yi masa daga Dubai zuwa Amurka.

Yadda kotun Amurka ta yanke wa Hushpuppi hukuncin ɗaurin shekaru 11.

“Abbas (Hushpuppi) ya kasance mutum ne mai nuna ƙwalisa da rayuwa ta ƙololuwar jin daɗi, sharholiya da almubazzaranci a soshiyal midiya. Ya kasance ya na facaka da kuɗaɗen da ya ke damfarar jama’a a ƙasashe daban-daban,” haka mai gabatar da ƙara Martin Estrada ya bayyana.

“Raymond Hushpuppi ya kasance ya sha damfara da ƙoƙarin damfarar Amurkawa da sauran wasu ‘yan ƙasashe daban-daban waɗanda tsautsayi ya faɗa kan su. Ya kasance a sahun farko kuma a ajin farko na tantangaryar ‘yan damfarar da su ka yi ƙaurin suna a duniya,” cewar Don Alway, Mataimakin Daraktan Hukumar FBI a birnin Los Angeles.

“Abbas ya riƙa amfani da shafinsa na soshiyal midiya ya na nuna irin rayuwar ƙololuwar jin daɗi da bushashar da ya ke yi, ta hanyar almubazzaranci da kuɗaɗen da ya damfari jama’a daban-daban.

“Wannan yanke hukunci da aka yi masa abu ne mai ɗimbin tarihi, wanda ya tabbata sakamakon dogon lokacin da aka ɗauka ana bincike ta hanyar haɗin guiwa da jami’an tsaro a ƙasashe daban-daban.

“Hukuncin da aka yanke wa Hushpuppi zai zama kakkausan darasi da gargaɗi a zukatan sauran ‘yan damfara a duk inda su ke cikin duniya cewa, FBI za ta zaƙulo su domin a hukunta su, kuma a ƙwatar wa waɗanda aka damfara haƙƙinsu.”

Laifukan da su ka janyo wa Hushpuppi ɗaurin shekaru 11 a Amurka:

  1. Ya haɗa baki da wani ɗan damfara mai suna Ghaleb Alaumary ɗan garin Mississauga a Kanada domin su karkatar da maqudan kuɗaɗen damfarar da su ka sata har a wasu bankuna ta hanyar satar amfani da fasaha, wato cyber-crime’.
  2. Cikin watan Janairu, 2019, Hushpuppi ya haɗa baki da Alaumary domin su karkatar da kuɗaɗen damfara daga wani banki a ƙasar Malta, ta hanyar ba shi bayanan waɗansu lambobin asusun ajiyar kuɗaɗe a wasu bankunan Romania da Bulgaria.

Amurka ta gano Hushpuppi ya haɗa baki ne da wasu ‘yan damfara domin a karkatar da kuɗaɗen ga gwamnatin Korea ta Arewa. Akwai ma wani ɗan Korea ta Arewa da aka danƙo, aka maka shi kotu.

  1. Raymond Abbas ya amince ya tafka asarar Dala miliyan 14.7 a harƙallar sa da bankin Malta.
  2. Cikin watan Mayu, 2019 Hushpuppi da Alaumary sun yi ƙoƙarin damfarar wani kulob ɗin ƙwallon ƙafar ƙwararru a Ingila, wanda su ka nemi a saka masu kuɗaɗen a wani bankin ƙasar Mexico.
  3. Cikin Oktoba 2019, Abbas Hushpuppi sun yi yunƙurin damfarar wani kamfanin lauyoyi maƙudan kuɗaɗe a nan Amurka, har Dala 922,857.
  4. An yi wa Alaumary shari’arsa daban, kuma an ɗaure shi shekaru 140, daidai da watanni 11 da rabi. Kuma an umarci ya biya waɗanda ya damfara haƙƙin su har Dala miliyan 30.
  5. Hushpuppi ya amsa laifinsa na yunƙurin haɗa baki shi da wasu domin damfarar wani Balaraben ƙasar Ƙatar Dala Miliyan 15, bisa nufin ya ba su kuɗin a gina makaranta ‘sadaƙatuj jariya’.
  6. Mai Shari’a Wright ya umarci Hushpuppi ya biya wani da ya damfara Dala 922,857 sai kuma wani ɗan kasuwa a ƙasar Ƙatar da kotu ta umarci Hushpuppi ya biya shi Dala 809,983.
  7. Abbas ya yi amfani da Dala 50,000 daga kuɗaɗen damfarar Balaraben Ƙatar ya samu bizar da ta ba shi iznin zama da kuma auren harƙalla da ya yi da wata mata.
  8. Cikin Janairu 2020, Hushpuppi tare da wani abokin harƙallarsa sun damfari ɗan kasuwa Dala miliyan 15. Sai dai kuma ɓalli ya tashi bayan sun rigaya sun karɓi Dala 575 a cikin kuxin.
  9. Hushpuppi ya furta da bakin sa da kuma a rubuce cewa a cikin watanni 18 an haɗa baki da shi an yi yunƙurin yin damfara ta aƙalla Dala miliyan 300.

Duk da dai wasu da dama daga cikin harƙallar ba su yi nasara ba, amma kuma hakan ya nuna irin zurfi da ƙarfin Hushpuppi a harkar damfarar jama’a.”