NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na kimanin Naira miliyan 200 a cikin watanni 10 a Jihar Kuros Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar NDLEA reshen Jihar Kuros Ribas ta kama muggan ƙwayoyi da suka kai Naira miliyan 200 daga watan Janairu zuwa Oktoba 2022.

Kwamandan hukumar na jihar Kupi Maulse ya sanar da haka ranar Litinin a garin Calabar.

Maulse ya ce hukumar ta kama muggan ƙwayoyin da suka haɗa da hodar ibilis gram 77.9, hodar ibilis ta mai nauyin ruwa gram 104.9, methamphetamine gram 23.4, ganyan wiwi kg 162.52 da wasu ƙwayoyin dake saka maye da har kilogiram 216.12 sannan jimlar su duka zai kai Naira miliyan 50.

Ya ce hukumar ta kuma ƙona gonakin wiwi guda biyu a dazukan Akamkpa da Odukpani masu faɗin hekta 15 sannan kuɗin ganyen wiwin da aka noma ya kai Naira miliyan 150.

Daga nan Maulse ya ce hukumar ta kama mutum 159 dake da alaƙa da sha ko safarar muggan ƙwayoyi a jihar.

Ya ce daga cikin waɗanda suka kama kotu ta yanke wa mutum 21 hukunci, hukumar na gudanar da bincike akan mutum shida sannan sauran na jiran babban kotu a jihar ta yanke musu hukunci.

Maulse ya ce rashin isassun motocin sintiri na daga cikin matsalolin dake hana hukumar gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Ya ce masu safarar muggan ƙwayoyi na tallar muggan ƙwayoyi a fili, siyar da ƙwayoyin a bakin rafi da filayen ƙwallon ƙafa.

Sauran wuraren da ake siyar da ƙwayoyin sun haɗa da gidajen mutane musamman a tsofaffin unguwani, ƙofar kulub sannan da amfani da waya domin yin odar ƙwayoyin domin a kawo wa mutum har gida.