Rundunar ‘yan sandan Borno ta tsare wata akuya bisa laifin cinye kifin sayarwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kamar yadda jami’in rundunar ‘yan sandan Jihar Borno Zagazola Makama, ya bayyana cewa wani mutum mai sana’ar sayar da kifi ya kawo ƙarar wata akuya cewa ta cinye masa tarin kifi da ya kasa don sayarwa.

A ƙarar da ya shigar ya ce wannan akuya ta fi shekara biyar tana yi masa ta’adi kuma ya sanar wa mai akuyar.

Ibrahim wanda akuyar ta yi masa ta’adi ya ce: ”A wannan rana, akuyar ta riƙa lallaɓowa tana fako na, ni ma kuma na ƙi matsawa. Amma kuma sai ta yi kamar ta tafi, ashe ta laɓe ne, daga tashi da na yi ‘yan mintoci sai ko ta diran ma kifin nan ta lamushe su tas.”

Ibrahim ya ƙara da cewa ta daɗe ta na yi masa ta’adi amma wannan da ta yi ya fi baƙanta masa rai domin ya yi asara mai yawan gaske ne.

Sai dai kuma Lubabatu Mohammed wadda ita ce mai akuyar, ta roki da a yi mata sassauci a saki akuyar, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta buga.

”Idan aka saki akuyar zan sayar da ita, ko in yanka ta mu cinye ko kuma in rika ɗaure ta wuri ɗaya,” inji ta.